Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ta bukaci al’ummar Musulmi da su fara laluben sabon watan Rajab na Kalandar Musulunci daga daren gobe na Juma’a.
A wata sanarwa da Majalisar ta fitar wacce ke karkashin jagorancin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ta ce Juma’ar ce za ta kasance 29 ga watan Jumadal Akhira wanda zai yi daidai da 12 ga watan Fabrairun 2021.
- Farfesan Jami’ar Tafawa Balewa ya kubuta daga hannun ’yan bindiga
- Yadda matasa ke neman rusa gadar da ta hada yankunan garin Jos
- Hadarin mota ya yi ajalin mutum 1, 8 sun jikkata a hanyar Kano zuwa Zariya
Sanarwar ta bukaci mutane da su kai rahoton ganin jaririn watan ga wani dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da sakon ganin jaririn watan ga Sarkin Musulmi.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Wazirin Fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce a a fara duban jijirin watan da zarar rana ta fadi.
Watan Rajab shi ne na bakwai a jerin watannin kalandar Musulunci ta Hijira, wanda daga shi sai na azumin Ramadana.