✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kwace shagunan magoya bayan IPOB —Matasan Arewa

Matasan Arewa sun bukaci a kwace kantunan magoya bayan IPOB a yankin har abada.

Matasan Arewacin Najeriya sun bukaci gwamnonin yankin su kwace shagunan duk masu goyon bayan kungiyar ’yan a-warren Biafra ta IPOB a yankin.

Matasan sun bayyana hakan ne a martaninsu ga umarnin IPOB ga mutanen yankin Arewa ta Tsakiya cewa su zauna a gida kar su bude harkokin kasuwancinsu a matsayin goyon baya ga kungiyar.

Sanarwar da kakakin Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, ya fitar ta ce, “Muna kira ga gwamnonin Arewa da su tabbartar cewa kngiyar ta’addanci ta IPOB ba ta shigo nan yankin ba.

“Sannan muna rokon gwamnonin sun tabbatar an kwace shagon duk wani dan Arewa da ya ki bude shagonsa saboda goyon bayan IPOB har abada.”

Ya ce Arewa ta dade da fahimtar muhimmancin kiyaye bin doka da oda wajen neman biyan bukatunta a karkashin tsarin dimokuradiyya, saboda haka ba za ta taba biye wa ’yan a fasa kowa ya rasa ba.

A cewar AYCF, tun da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas sun gamsu da abin da IPOB take yi a yankinsu, idan sun ga dama su shekara 10 suna  ci gaba da zama a gida yadda kungiyar take so, babu abin da ya dami Arewa.

Amma kuma Arewa ba za zura ido IPOB ta shigo da kowace fuska ba tana neman yamutsa hazo a Jihohin Arewa ta Tsakiya da suka hada da Kogi, Neja, Filato, Binuwa da sauransu ba, saboda matsalolin tsaron da ke gaban jihohin ma kadai sun ishe su.

ACF ta soki matakin yin kone-kone ko kashe-kashe da sunan neman biyan bukata, wanda hakan ya saba wa tsarin dimokuradiyya.

Don haka ta bukaci jama’ar Arewa da su guji duk wani yunkuri na tayar da fitina.