Muhammad Garba Kabara na cikin sahu na biyu wurin kafa masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood, a yanzu an daina jin duriyarsa, shin ya bar harkar ne? Ya kuma yi bayanin matsalolin da suka yi cacukwi da masana’antar, inda ya ce harkar kullum baya take ci maimakon gaba. Ga yadda hirar ta kasance:
Za mu fara da tarihinka a takaice..
Sunana Muhammad Garba Kabara, a harkar fim kuwa kusan muna daga cikin shigowa ta biyu, daga wanda suka fara assasata sai mu, a lokacin da na shigo harka na fara da mai taimaka wa mai daukar hoto, daga nan na zama mai daukar hoto, sai likafa ta ci gaba na zama mai ba da umarni duk a wancan lokaci.
A matsayinka na tsohon darakta wanda tun wannan masana’antar ba ta bunkasa ba, kuka yi gwagwarmaya a cikinta, to me ya kawo bayan harka ta samu daukaka sai aka daina ganinka, ko ka daina harkar ne?
To ka san harkar shirya fina-finan Hausa tana da fadi, kuma kowa yana da nasa lokaci, idan ana yi da kai yau, gobe sai ta juya ga wani, to idan ta juya ga wani sai a ga kamar ba ka cikin harkar ne. Idan ka duba tun farkon harkar akwai wadanda suka fara amma yanzu ba su ba ne wasu ne daban. Wannan shi ne dalili ba wai dainawa muka yi ba.
A yanzu masu kallon fina-finai suna korafe-korafen daraktoci kun bar ’yan wasa na fadar kalmomin da suka ga dama wadanda suka saba wa addini da al’adar Hausawa, ko me za ka ce kan haka?
To, a gaskiya akwai matsaloli da yawan gaske, domin idan ka auna daraktocin da da na yanzu ba dai suke ba, ba wai ina nufin na baya sun fi na yanzu komai ba, a’a abin da nake nufi mafi yawan masu ba da umarni a fina-finan Hausa a yau ba karatu suka yi ba, kawai na gani ana yi ne, amma daraktocin da mafi yawansu sun yi karatun harkar, wasu kuma sun samu alaka ta kut-da-kut da wadanda suka iya aikin, sun san abin da ake nufi da daraktin, ba wai kawai ‘action’ ba, shi ne daraktin. Wannan dalilin yana daya daga cikin abin da ya haddasa mana koma baya a cikin harkar fim. Ina mamakin jin ana cewa fim din Hausa na ci gaba, babu wani ci gaba, sai dai baya ake ci, dalilina shi ne an samu ci gaban ‘technikue’ wata kila a ce kyamara da ake amfani da ita ba irin ta da ba ce, kyunfutar yanzu ba daya ba ce da ta da, ko muna so ko ba ma so zamani ne ya zo dole a yi wannan, amma idan ka dauko fina-finan baya ka dauko na yanzu ai akwai banbamci sosai a bangaren labarai da zamantakewa. Ga shi yanzu kana fadar ‘yan kallo suna kukan ana barin ‘yan wasa na fadar kalmomi san ransu, ka ga abin da wannan ya nuna gaba daya ya kamata a samu wayar da kai musamman ga wadanda harkar ke tafiya da su, domin harkar daraktin ba harka ce ta jahilci ba, dole sai ka nemi ilmin abin sa’annan ka koyar, ya kamata su san su malamai ne to ya za su koyar ba su da ilmin abin. Akwai matsala gaskiya babba, abin da ake so duk abin da za ka yi kana da ilmi a kansa, ba daidai ba ne ba ka san abu ba kuma kana sanar da mutane. Masana’antar fim tana dauko wanda ta ga dama, idan kana dako ko dinki sai ka samu sa’a ka yi fim da ya yi fice, shi ke nan sai a ga ba wani da ya fi ka a harkar, kuma komai ba ka sani ba, duk abin da aka dauko a harkar fim sai a kawo maka, kai ko idan ka tashi yin fim ba bincike da tuntubar na gaba da kai a harkar, sai ya yi gaban kansa, saboda tunanin ya fi kowa iyawa, wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka dakile harkar kuma idan ba a yi maganin abin ba har abada haka za a tsaya, kullum baya za a yi.
Wace shawara za ka ba daraktoci na yanzu wadanda kake ganin idan suka bi su za su kaucewa korafe-korafen da ‘yan kallo ke yi a yanzu?To ka san a lokacin da harkar ke yi da mutum ba kasafai yake hangen irin wadannan abubuwan ba, sai ta a jiye shi sai ya duba, shawara aka ce daukar daki, to guda daya ce idan ba ka sani ba to ka tashi ka koya, amma magana ta gaskiya ba wai bakin ciki kake wa mutum ba ko so kake ya ci baya ba, duk abin da za ka yi saboda bunkasa harkar, to ya kamata ka nemi ilmin abin sai ka zo ka rika yi, ta haka ne za ka rika shigar da abin da ya kamata har jama’a su gamsu da shi. Ba na mantawa na taba zuwa Sakkwato in yi wani fim mai suna ‘Li’ani’ da muka zo muna bincike kansa sai da muka ajiye aiki kwana uku, ba mu yi shutin ba, idan ka ci karo da abin da ba ka sani ba ya kamata ka tambayi masana abin da shawararsu in ka yi haka na tabbata ba za a ji kunya ba. Kuma za a daina kuka da mu. Za mu daina samun matsala, ni kaina na samu matsaloli da yawa a cikin Kano, saboda halayyar wasu daga cikinmu, za ka ga an saki fastoci da ttireloli marasa kyawu, in muka yi magana wasu su ce ai bakin ciki muke yi masu. Muna kokari kada wani abu ya zo.
Babu wata hukuma da ke kula da harkokin fina-finan Hausa da har yanzu aka kasa magance matsalolin?
A gaskiya akwai hukuma, amma tana da tata matsala, wato idan aka ce an kafa hukumar tace fina-finai to ya kamata ta zauna ta yi nazari, ta kuma samu wadanda ke cikin harkar sosai ta nemi shawarwarinsu. Mafi yawan abin da ake yi shi ne ka ga an nada ka shugaba sai kawai ka yanke hukunci ga yadda za ka yi ka yi maganin matsalar, sai kaki samun nasara saboda mai daki ya san inda yake yi masa zuba, da dama aka shigo wurin a gyara sai a bata, ita harkar fim kamar harka ce ta sadarwa, tare irin wadannan abubuwa abu ne mai wahala a lokaci guda ko da karfi, ba zai yiwu ba, na sha fada musu akwai lokacin da Malam Rabo ya hada mu da wasu malamai aka yi ta mujadala a kan na ce duk abin da Rabo yake yi baya ake ci, don ba a fada da sadarwa, sai dai a nemo hanyar ingantata. Matakin da ya kamata a dauka ba shi ake dauka ba, don haka hukuma na taka rawa wurin kara lalacewar lamurran. Sa’annan ‘yan kallo musamman masu saya su gani su ma suna taka rawar kara gurbacewar harkar a duk lokacin da ka sanya kudinka da yawa ka yi fim mai inganci don ka fadakar da al’umma to wallahi sai ka tafka asara, da zarar ka yi wanda zai gurbata al’umma, to sai ka samu riba ninki ba ninki. Hanyar da nake ganin ya dace a bi, hukuma ta rika tace fim da gaskiya ba sani ba sabo, mu kuma ‘yan fim kada mu ketare iyakokin Allah, don gudun da-na-sani a gaba, ‘yan kallo su rika duba kowane fim ana rubuta masa 18 ko G. G na nufin kowa da kowa na iya kalla, karami da babba, amma idan aka sanya 18 sai wadanda suka balaga ke nan.
Wace irin shawara gare ka ga ‘yan uwanka daraktoci?
A harkar fim darakta ne kashin-bayan komai, da zarar ya lalace to harkar ma ta samu matsala, don haka ya zama wajibi idan za ka yi daraktin ka sa ilmin abin da za ka yi, idan sai mai daukar hoto ya shirya maka komai, to gaskiya ban ga dalilin da za ka rika kiran kanka darakta ba, don ko makaranta ka je ana koyar da ke ilmin darakta aka ce idan aka rubuta labari ka bi shi yadda aka ce to kai ba mai ba da umarni ba ne, ka mayar wa mai labari labarinsa kai ba darakta ba ne. Lallai ya kamata a ce yana ilmi domin sanin abin da yake yi, ina ba da shawara mu dage mu nemi ilmi.