✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Jibril Aminu, ya rasu

Tsohon malamin makaranta, dan siyasa kuma ambasada, Farfesa Jibril Aminu ya rasu yana da shekara 85.

Tsohon malamin makaranta, dan siyasa kuma ambasada, Farfesa Jibril Aminu ya rasu yana da shekara 85.

Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar, kuma Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na jihar Adamawa, Hon Abdullahi Prambe ma ya tabbatar da haka.

Ya ce, “Ba za a taba mantawa da gudunmawar shi ba musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma shugabanci.”

Wata majiya da ke da kusanci da mamacin ta ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a Masallacin Kasa da ke Abuja.

Sai dai kawo yanzu, iyalai da ’yan uwan mamaci bas u fid da cikakken bayani kan yadda za a yi jana’izar mamacin ba ko kuma musabbabin rasuwarsa.

An haifi Farfesa Jibril Aminu a garin Song na jihar ta Adamawa a shekara ta 1939, kuma ya rike mukamai da dama a Najeriya.

Daga cikin mukaman da ya rike akwai Ministan Ilimi da Ministan Man Fetur da Jakadan Najeriya a Amurka sannan ya taba zama Sanatan Adamawa ta Tsakiya.

Bugu da kari, Farfesa Jibril kwararren likitan zuciya ne da ya jima yana bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasa a fannoni daban-daban.