Yawan sakin aure da ake fama da shi a kasar Saudiyya ya kai 127 a kowace rana, ko kuma biyar a kowace sa’a guda, kamar yadda alkaluman bincike suka kididdige.
Rahoton dai wata kididdiga ce da babban ofishin tara bayanan kididdiga (GAS) ya fayyace.
A cewar rahoton, an samu rabuwkar aure kimanin dubu 157 a shekarar da ta wuce.
Rahoton ya yi nuni da cewa, a bara sakin auren ya ragu in an kwatanta da shekarar da ta gabace ta, inda adadin ya haura da mace-macen aure har dubu 54. A Lardin Gabashi da Tabuk an samu yawan sakin aure da kashi 36.7 da 36.1 cikin 100. A Riyadh, yawan sakin auren ya kai kashi 31 cikin 100, inda a Jazan aka samu rabuwar aure da kashi 17.9 cikin 100.
Shugabar Hukumar Daraktocin daukar nauyin marasa galihu ta Mawadah, Gimbiya Sarah bint Musaed, ta bayyana cewa kimanin kashi daya bisa hudu na auren da ake yi a Saudiyya yana karewa ne da saki, inda ta yi nuni da cewa kimanin kashi 60 cikin 100 na sakin auren da ake yi na aukuwa ne a shekarar farko na auren.
Yawan al’umma kasar Saudiyya sun kai mutum miliyan 28 da dubu 830, bisa alkaluman kididdigar da aka tattara a shekarar 2013.
A kowace sa’a ana sakin mata biyar a Saudiyya
Yawan sakin aure da ake fama da shi a kasar Saudiyya ya kai 127 a kowace rana, ko kuma biyar a kowace sa’a guda, kamar…