✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu-Shettima: Lalong Ya Yi Katobara Da Sunan Fafaroma —’Yan Katolika

CCN ta nemi a hukunta Lalong kan batanci ga fafaroma, shi kuma ya ce girmama shugaban na Katolika ya yi

Wasu mabiya darikar Kotolika sun bukaci cocinsu ya hanzarta korar Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, saboda kalamansa siyasara da ya ambaci sunan Fafaroma.

Kungiyar ’Yan Kotolika ta Najeria (CCN), ta ce ambaton Fafaroma da ya yi, cin mutunci ne, domin babu abin da ya hada shugaban darikarsu da kuma cocinsu da siyasa.

“Lalong ya san Cocin Katolika babu ruwansa da siyasa, amma ya je yake ambaton Fafaroma domin kafa hujja da karbar mukami a siyasarsa, wanda batanci ne ga cocin a Najeria da duniya, da kuma martabar Fafaroma,” in ji shugaban CCN, Ben Amodu.

Don haka, ya ce wajibi ne gwamnan ya tuba, ya nemi gafarar wannan babban zunubin da ya aikata.

Ya yi kalaman ne a matsayin raddi, bayan Lalong, jagoran kamfe na dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, duk Musulmi, ya ce fafaroma bai hana shi karbar mukamin ba.

Ya bayyana cewa suna ci gaba da ganawa da fafaroma a idabar dare, kuma bai hana shi karbar mukamin ba, don haka yana mamakamin Kiristocin da ke sukar sa saboda karbar mukamin.

Gwamnan ya ce a matsayinsa na cikakken dan Katolika wanda aka yi wa bastisma kuma ya yi makatanar ’yan mishan, yana alfahari da jagoranytar yakin neman zaben Musulmi.

Sai dai mabiya darikar sun ce babbar katobara ce amabaton fafaroma da ya yi kan mukamin da aka ba shi na jagorantar yakin zaben Tinubu da Shetima, duk Musulmi.

A kan haka ne Ben Amodu ya yi kira da shugabanin Katolika da sauran masu fada a ji a darikar a Najeriya da su tabbatar sun hukunta gwamnan saboda ambaton fafaroma a kalamansa, laifin da sai ya yi kaffara a kai.

Amma a martaninsa, gwamnan ta hannun kakakinsa, ya ce ambaton fafaroma da ya yi girmamawa ce.

Ya kara da cewa yana nan a matsayinsa na Kirista mai biyayya ga Cocin Katolika.