Dattawan Arewa a Najeriya sun bukaci Shugaba Buhari ya gaggautar korar Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola.
Dattawan sun ce yin hakan ya zama wajibi saboda halin ko-in-kula da ministan ke nunawa wurin kammala ayyuka a yankin na Arewa.
Wani mamba Kungiyar Dattawa Arewa (NEF) Alhaji Rufai Mukhtar Danmaje, a tattaunawarsa da manema labarai ya yi zargin cewa babu aiki ko guda daya da Fashola ya kammala a yankin a shugabancinsa a ma’aiaktar.
“Dubi batun tashar lantarki ta Mambila inda ministan ya dauki lokaci yana yaudarar Shugaban Kasa da ‘yan Najeriya cewa aikin ya yi nisa, sai daga baya kwamiti ya bankado ashe babu abin da aka yi”.
“Babu aikin hanya ko daya a fadin Arewa da Fashola ya kammala; hatta hanyar Kano, Kaduna, Abuja, mai muhimmanci, wai ba za a kammala ba sai bayan mulkinsu, to me yake nufi”
“Wannan kadai ya isa a sallame shi; idan ma a wuraren da aka san abin da ya kamata ne, shi da kansa zai ajiye aiki”, inji shi.
A cewarsa: “Buhari ya rungume su ya ba su muhimman mukamai, suna yin ayyuka a yankunansu amma suna bakin cikin ganin an yi na Arewa.
“Ya kamata Shugaban Kasa ya kafa kwamitin tantace yanayin aiwatar da ayyuka”, kamar yadda ya ce.
Shugabancin karba-karba
Game da karba-karba na shugabancin Najeriya da Fashola da wasu ke yi, Alhaji Rufai cewa ya yi: “Wannan kadai ya isa fusata Arewa ta ki amincewa saboda ta gano cewa ba a yi mata adalci ba ta kowace fuska.
“Wannan fahimtar juna ce tsakaninsu kuma bai shafe mu ba; su suka yi abin su, amma mu ke zabe, saboda haka ya rage wa kowanne cikin mu da su ya yi abin da yake so.
“Muna sane da duk abubuwan da suke mana, mu ba dolaye ba ne da zai rika yi mana haka kuma ya yi tunanin mu goyi bayansa”, inji shi.