✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A kori duk jami’in gidan yari da bai iya harbin kisa ba —Minista

Aregbesola ya ce daga yanzu duk wanda ya kai hari gidan yari, to kada a bata lokaci wajen aika shi lahira.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ba da umarnin sallamar duk jami’in hukumar gidajen yarin da bai kware wajen harbin kisa ba.

Aregbesola ya ce daga yanzu duk wanda ya kai hari gidan yari, to kada a bata lokaci wajen aika shi lahira.

Harbewa a kashe shi ya kamaci masu kai hari a gidajen yari, “Ba rauni ya kamata a ji musu ba, don haka duk jami’in da bai iya harbi ya kashe ba, to in ba za ku kore shi ba, ku mayar da shi gidan yarin mata,” in ji ministan.

Ya ce daga yanzu an sanya dokar ta baci a gidajen yari, duk wanda ya kai musu hari ko ya nemi yi musu kutse, to a harbe shi har lahira.

Ya sanar da haka ne a taron kaddamar da sabon tambarin Hukumar da gidajen ma’aikata da kuma cibiyar fasahar sadarwa ta zamani a hedikwatar hukumar.

Ministan ya kuma karrama wasu jami’an hukumar guda 25 da suka dakile harin da aka kai gidan yari a Jihar Neja.

A yayin karramawar, Aregbesola ya nuna takaicinsa kan yadda jami’an hukumar a wasu gidajen yarin suka nuna tsoro a lokacin da aka kai wa wuraren hari.

Ya ce, “Bindigogin da ke hannunku ba kayan wasa ba ne, amfaninsu shi ne yin kisa.

“Duk jami’in da bai iya harbin kisa ba da duk wani matsoraci a sallame shi, ko a je a ba shi horo.

“Dole ne duk jami’in da za a kai matsakaici ko babban gidan yari ya kasance mutum mai zafi.

“Abubuwan kunya da suka faru a gidajen yarinmu sun yi yawa, dole kuma su dakata haka,” in ji shi.

A cewarsa, yawancin bata-garin da suka hana al’ummar yankin Kudu maso Gabas sakat, musamman a  Imo, gudaddun ’yan gidajen yarin da ke jihar ne.