Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA) ta ce Gwamnatin Najeriya na da kyakkyawar manufa a yunkurinta na shigo da rigakafin cutar COVID-19 kafin karshen watan Fabrairun 2021.
Babban Daraktan hukumar, Dakta Faisal Shu’aibu ne ya bayyana hakan yayi wani taro da aka shirya wa masu ruwa da tsaki kan harkokin kafafen watsa labarai a kan sabuwar allurar rigakafin da ya gudana ta fasahar bidiyo.
Dakta Faisal, wanda ya ce rigakafin a yanzu ita ce sabuwar garkuwa daga cutar a duniya.
A cewarsa, “Wanna rigakafin na da matukar amfani kuma tuni Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tantance sahihancinta, za ta sami sahalewar Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) domin tabbatar da dakile yaduwar cutar a Najeriya.
“A zangon farko na rigakafin, za mu ba da fifiko ga ma’aikatan lafiya saboda sune suka fi yin mu’amala ta kai tsaye da masu dauke da cutar a asibitoci da kuma wuraren killace mutane,” inji shi.
Ya ce zai so ganin an fara yi wa Shugaban Kasa, Mataimakinsa, da Sakataren Gwamnatin Tarayya da sauran kusoshin gwamnati rigakafin a idon jama’a don tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa ba ta da wata illa.
“Akwai hujjar da take nuna cewa idan aka yi wa mutum rigakafin, akwai yuwuwar ya sami karin karfin garkuwar jiki da kuma kare wasu ma daga kamuwa da ita,” inji Dakta Faisal.