✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karshe Gwamnatin Tinubu ta amince tana biyan tallafin fetur

Ana hasashen kashe kuɗaɗen tallafin mai zai kai tiriliyan Naira ₦5.4 a ƙarshen shekarar 2024.

An yi hasashen tallafin man fetur zai lakume kimanin Naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024, a cewar Gwamnatin Tarayya.

Wannan ya saba wa Naira tiriliyan 3.6 da aka ware wa tallafin man a kasafin kudin shekarar 2023.

Wani daftarin rahoton shirin inganta ayyuka sufuri da sadarwa (ASAP) wanda Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya gabatar wa Shugaba Tinubu a ranar Talata, ya nuna an biya kudaden tallafin mai na Naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 Naira tiriliyan 5.4, wanda ya haura na 2023 da Naira tiriliyan 1.8.

An tsara shirin ASAP ne don magance manyan kalubalen da suka shafi yunkurin yin gyare-gyare da habaka cigaba a sassa daban-daban na tattalin arziki.

“A halin yanzu, ana hasashen biyan kudaden tallafin mai da zai kai Naira tiriliyan 5.4 a karshen shekarar 2024.

Wannan ya haura ₦3.6 tiriliyan da aka kashe a 2023 da kuma ₦2.0 tiriliyan da aka biya a 2022,” in ji daftarin shirin ASAP da Edun ta gabatar.

A baya dai, Gwamnatin Tinubu ta tsaya tsayin daka cewa ba za ta kara ba da tallafin man fetur ba.

A watan Disamba, gwamnatin ta ce sabanin ikirarin da Bankin Duniya ya yi na cewa ta ci gaba da biyan tallafin,  zamanin tallafin mai a kasar ya wuce”.

Da yake magana a wata tattaunawa da tashar Talabijin Channels TV, Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ya ce shugaba Tinubu ya bayyana ƙarara tun daga ranar farko da ya hau mulki cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin mai ba.

Ministan ya ce, cire tallafin ya kawo karin kudaden shiga a asusun tarayya.

A watan Afrilu, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i, ya ce Gwamnatin Tarayya na kashe kuɗaɗen tallafin man fetur fiye da da.