Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sanar da cewa ta gudanar da gwajin makami mai linzami mai gudun walkiya a cikin nasara.
Amurka ta sanar da gwajin makamin ne a ranar Laraba bayan tuni kasashen Rasha da China sun yi gaba a fannin kera makamai masu gudun walkiya.
- Ba abin da zan bar wa ’ya’yana gado in na mutu – Buhari
- Najeriya na neman diyyar ‘gurbataccen abincin’ da aka ba alhazanta a Saudiyya
Nasarar gwajin makamin da cibiyar binciken tsaron Amurka ta yi na makamin da kamfanin kera makamai na Lockheed Martin ya kera na zuwa ne mako biyu bayan rashin nasarar wani gwajin.
Duk da haka ana ganin makamai masu gudun walkiya da Rasha da China suka mallaka babu kamarsu a duniya.
Amurka wadda ke zaman doya da manja da kasashen Rasha da China dai ta shiga damuwa ganin yadda kishiyoyin nata suka shige mata gaba a bangaren mallakar makamai masu gudun walkiya.