✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A karo na 2 cikin kwana 5, bam ya sake fashewa a kauyen Neja

Wannan shi ne karo na biyu da bam din ke tashi a yankin cikin kwana biyar.

Wani abu da ake kyautata zaton bam ne ya sake fashewa ranar Juma’a a kauyen Galadiman-Kogo da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Fashewar na zuwa ne kwana biyar da tashin wani bam din a yankin, wanda ya yi sanadin rasuwar jami’an Hukumar tsaro ta NSCDC su hudu.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin zai kira daga baya.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kira ba.

Kazalika, wayar Kwamishinan Kananan Hukumomi, Masarautun Gargajiya da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, ta kasance ba ta tafiya, kuma bai amsa rubutaccen sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya tura masa ba.

Aminiya ta gano cewa bam din ya tashi ne wajen misalin karfe 7:00 na yammacin Juma’a.

Sani Abubakar Yusuf Kokki, Shugaban Kungiyar masu kishin Shiroro, ya ce, “Wani abu da muke tunanin bam ne ya tashi yanzun nan a yankin Galadiman-Kogo na Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.”