✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A kan idon sojoji ’yan bindiga suka sace mana mutum 50’

Maharan sun shafe tsawon awa biyu suna cin karensu ba babbaka.

Akalla mutum 50 ne ’yan bindiga suka sace a kauyen Ruwan Godiya da ke Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina, bayan wani hari da suka kai.

Wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa sai da maharan kusan su 60 suka yi dandazo a kauyen a bisa babura sannan suka fara harbi a iska, inda suka shafe awa biyu suna cin karensu babu babbaka.

Ya ce a lokacin da maharan suka kai wa kauyen farmaki, akwai dakarun soji kusan 20 amma abin mamaki sojojin sun gaza yin wani katabus.

“Tun kafin zuwan maharan muka samu labarin shirinsu na kawo mana hari kuma mun sanar da jami’an tsaro, amma duk da haka sai suka shigo mana da misalin karfe 7:30 na dare suka shafe awa biyu suna barna.

“Sun raunata mutum uku da harbin bindiga amma babu wanda ya rasa ransa, sai dai sun yi awon gaba da sama da mutum 50 suka kuma sace mana kayan amfani,” a cewarsa.

Kazalika, wani mazaunin kauyen ya ce wasu sojoji sun ga lokacin da maharan suke tserewa da mutanen da suka sace daga kauyen, amma sun gaza dakatar da maharan.

Wannan na zuwa ne washegarin da wasu ’yan bindiga kai hari a Kasuwar Yandaka da ke Karamar Hukumar Batsari a jihar, suka yi awon gaba da daukacin dabbobin da ke kasuwar.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba sun kai hari a kauyen Illela inda suka kashe mutum 12, wasu da dama kuma suka bace.

Harin da ya sanya mutanen kauyen Illela daukar makamai tare da yakar ’yan bindigar da suka kai musu farmaki, kamar yadda jami’an tsaron jihar suka bayyana.