✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kalubalanci miyagun tsare-tsaren Buhari –’Yan Kwadago

Gammayar kungiyoyin kwadago sun bukaci a mayar da farashin fetur akalla Naira 87

Gamayyar Kungiyoyin Kwadago karkashin inuwar JAF ta shawarci ’yan Najeriya kar su amince da duk tsarin da Gwamnatin Buhari ta fito da shi da ba zai amfani mutanen Najeriya ba.

Kungiyoyin da suke karkashin gammayar sun hada da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da LASCO wato (Labour and Civil Society Coalition) da kuma TUC (Trade Union Congress).

Gamayyar Kungiyoyin ta zargi gwamnati mai ci da yaudara da kuma yada farfaganda.

Shugaban tsare-tsaren Kungiyar Farfesa Ademola Aremu, a ganawarsa da manema labarai a Ibadan, Jihar Oyo, ya nuna rashin gamsuwa da yadda ’yan Najeriya ke fama kan karin kudin fetur da wutar lantarki da harajin kayayyaki da wasu tsare-tsaren da ke cutar da mutane wanda gwamnatin take yi.

Aremu, ya yi kira ga jama’ar Najeriya da su ba su hadin kai wurin yakar rashin adalcin da ake yi wa ’yan Najeriya ta hanyar gudanar da gagarumin gangamin neman gwamnati ta soke munanan tsare-tsaren da take fitowa da su.

“Muna Allah wadai ga karin kudin fetur na farshin lantarki da harajin kayayyaki da wasu tsare-tsare masu cutar da jama’a da Gwamnatin Buhari ke kakaba wa jama’a; muna kiran ’yan Najeriya da su nuna rashin amincewarsu har sai an soke wadannan kare-kare.

“Muna kira da a soke kare-karen da aka yi wanda ya hada da fetur da lantarki da harajin kayayyaki. Akalla a dawo da farashin mai yadda yake a 2016 na Naira 87, sannan a gyara tsoffin matatun mai na gwamnati a kuma gina sabbi ta yadda ’yan Najeriya za su sharbi romon dimokuradiyya.

“Kazalika a daina sayar da kadarorin gwamnati sannan a bar bangaren mai a karkashin gwamnatin”, inji kungiyar.