Majalisar Kula da Kafofin Watsa Labarai ta Kasa (NCI) ta kawo shawarar a kafa Hukumar Kula Kafofin Watsa Labarai na Intanet don tace labaran da kafafen sadarwa zamani suke yadawa a Intanet.
Majalisar ta kawo shawarar ce a takardar bayan taronta na kasa da ta gudanar a Jos fadar Jihar Filato a ranar Juma’ar da ta gabata, kan yadda za a magance labaran karya da kalaman batanci da ake yadawa a kafafen sada zumunta a Najeriya.
Majalisar wadda ta gudanar da taron a karkashin jagorancin Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ta ce mafiya yawan kafafen labaran da suke amfani da kafafen sada zumunta, labaran da suke turawa a Intanet a Nijeriya, ba su sanya addireshinsu kuma ba sa tantance labaran da suke turawa. Majalisar ta kuma shawarci manyan jami’an watsa labarai na jihohin kasar nan, su bude shafukan da za su rika karyata duk wasu labaran karya ko maganganun batanci da irin wadannan kafofin watsa labarai suka tura a Intanet.
Majalisar ta ce ganin irin yadda ’yan Najeriya suka yi imani da irin wadancan kafafen watsa labarai na Intanet, mukatar ba a tashi tsaye an magance miyagun ayyukan da suke gudanarwa ba, za su iya kawo matsala a zaben shekarar 2019.
Majalisar ta umarci Ma’aikatar Watsa Labarai ta Tarayya da takwarorinta na jihohi su tashi tsaye wajen bayar sakonnin zaman lafiya da hada kan jama’a da kuma yi wa jama’a bayani kan illolin labaran karya da kalaman batanci.
Taron wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Filato, Farfesa Sonni Tyoden ya bude, kuma aka gudanar da shi a karkashin jagorancin Minista Lai Mohammed ya samu halartar kwamishinoni da manyan sakatarorin ma’aikatun watsa labarai na jihohin kasar nan.