Kungiyar Tabbatar da Jituwa Tsakanin Addinai ta IDFP ta bayyana bakin ciki da damuwarta kan yadda abin jiya ke neman dawowa game da hare-hare a Jihar Kaduna, musamman a Kudancin jihar da Birnin Gwari, inda ta bukaci a rika gaggauta hukunta duk wadanda aka kama da laifi.
IDFP ta ce duk da cewa an dade ana fama da irin wannan matsalar a jihar, an samu karin faruwar lamarin a ’yan kwanakin nan, wanda hakan ya jawo rasa rayuka da dimbin dukiya.
“Yanzu haka Kudancin Kaduna ne ya fi fama da matsalar hare-haren, wanda hakan ya jawo cece-kuce na kalaman batanci na kabilanci da daukar alwashi a bayyane da sauransu.”
Da take jajanta wa wadanda hare-haren ya shafa, kungiyar ta bukaci kowane bangare ya mayar da kubensa ta hanyar rungumar sulhu da zaman lafiya.
Wannan bayanin yana kunshe a wata takarda da kungiyar ta fitar tare da sa hannun shugabanninta Alhaji Kunle Sani da Bishop Sunday Onuoha.
Kungiyar ta kara da cewa, “ya kamata a kara tsaro musamman a yankunan da aka fi samun matsalar, tare da yin aiki da kungiyoyin tsaro na yankunan domin saukake aikin.
“Muna kuma kira da a ba kowane bangare damarmakin da suka cancanta domin magance matsalar rashin aikin yi. Sannan ya kamata gwamnati da jami’an tsaro su rika gudanar da ayyyukansu a fili musamman wajen hukunta duk wadanda aka kama da laifin tayar da zaune tsaye domin ya zama izina ga wasu.”
A karshe kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen tattara bayanan sirri ta hanyar yin aiki da kungiyoyin tsaro na unguwanni.
Ta kuma bukaci dukan ’yan Najeriya da su hada hannu da gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya.