✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A hannun Shekarau da Kwankwaso aka lalata siyasar Kano (2)

Sakamakon wadannan abubuwa da Kwankwaso da Shekarau suka yi a baya, yau an wayi gari saboda lalacewar siyasa a Kano, kowa tsoron tsayawa takarar gwamna…

Sakamakon wadannan abubuwa da Kwankwaso da Shekarau suka yi a baya, yau an wayi gari saboda lalacewar siyasa a Kano, kowa tsoron tsayawa takarar gwamna a kashin kansa yake yi, domin in dai ba gwamna ko jagoran jam’iyya mai ci ne ya tsayar da shi ba to wai bata lokacinsa ya ke yi. Kuma komai nagartarka, ba za a taba samar da yanayin da za ka iya wata takarar kirki da dan lelen gwamna ba.
Duk da cewa a lokacin SDP da NRC, mutane da yawa na da ra’ayin cewar an yi murdiya a zaben gwamna tsakanin Injiniya Magaji Abdullahi da Gwamna Kabiru Gaya; to amma wannan ma wasan yara ne a kan abin da muke gani a yanzu. Mafi yawan zaben cike gurbi da aka yi a karkashin mulkinsu ba su da inganci. Tun daga zaben cike gurbin dan majalisar Jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa a shekarar 2006, har zuwa zaben cike gurbi na ‘yan majalisun Kano ma su wakiltar Gaya da Garko da aka yi a shekarar 2013.
A shekarar 2007 ne, gwamnatin Mallam Shekarau ta shirya zaben kananan hukumomi mafi muni a tarihin siyasar Kano, inda kirikiri musanya sunayen wadanda aka sanar sun ci zabe a filin zabe da sunan abokan takararsu a wani wajen daban ko a wani lokacin daban, wannan zabe ya yi muni kwarai.
kasa da makonni biyu da suka gabata, Gwamnatin Kwankwaso ta shirya wani zaben mummuna irinsa, wai da sunan ta rama abin da Shekarau ya yi mata. A wannan almara mai kama da zabe, an ayyana cewar jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun kansiloli 484 da ciyamomi 44 a Kano. To yanzu, mene ne abin burgewa a nan a ce babu adawa ko daya, kuma bayan kowa ya san hakan ba zai yiwu ba a Kano?
Da alama dai an saka talakawan Kano a tsakiya ana wasan kwallon kafa da su. Wannan ya sa su su shiga rana su hau layi don zabar ra’ayinsu, sai kuma a fadi sakamakon da aka ga dama, sannan wancan ma ya aikata irin hakan wai sannan ya ce ai ramawa ya yi. Talakawan Kano su ne abin ya ke karewa a kansu kuma abin takaici wai shugabanninsu su ke mu su haka.
A lokutan mulkin Shekarau da Kwankwaso, babu wanda yake da ikon ya zama shugaban jam’iyyar da suke ciki sai wanda suke so, kuma shugabannin jam’iyya ba su da wani ‘yancin kansu sai dai ra’ayin gwamnati, domin ta mayar da su jami’anta. Idan mutum yana takara da gwamna ko dan lelen gwamna, shugabanni ba za su zama alkalai ma su adalci ba, karara za su nuna maka kai ba ma dan jam’iyyar ba ne ko kuma ka ma yi laifi da ka tsaya takara da gwamna. Mu a da sai dai mu ji labarin irin wannan abin takaicin a wasu jihohin amma ba dai a Kano ba.
A dalilin haka, yau mun wayi gari, gwamnoni su suke nada shugabannin  jam’iyya, kuma ba su da wani amfani. Da ka nemi shawararsu ma, gara ka tunkari gwamnan mai mulki kai tsaye domin aikinsa kawai su ke yi ba na jam’iyya ba. Ya kamata wadannan jagorori su koyi darasin da tarihin siyasarsu ya koya mu su. Su tuna cewar sun samu dama kuma sun rasa ta.
A gaskiya duk da cewa Injiniya Kwankwaso da Mallam Shekarau sun bai wa Kano gudunmawa a gwamnatance, amma kuma sun kawo tarnaki ga tsarin da ta hanyar sa ne kawai za a iya samun wasu irinsu su bullo su masu bayar da tasu irin gudunmawar. Yadda tsarin siyasa ya fito da su aka sansu, jama’ar Kano suka karbe su kuma har suka samu dama, to su ma su kyale adalci ya tabbata a tsarin domin kowa ya samu dama ba tare da tsangwama ba. Har yanzu akwai dama a hannunsu domin su ne suke haska fitilar siyasar Kano har gobe. Idan suka bari wannan dama ta subuce daga hannunsu cikin wannan yanayi ba tare da sun gyara ba, to tarihi ba zai taba yafe mu su ba, domin kuwa ba za a rika tunawa da su, irin tunawar da ake yi wa Mallam Aminu Kano ba. Mallam Aminu Kano ya samu babbar damar sa ne wajen yin jagoranci, Shekarau da Kwankwaso sun samu damar yin mulki a gwamnatance da kuma jagoranci a siyasance baki daya.
Mallam Amir, Shugaban kungiyar Foundation for Better Initiatibes (FBI), ya rubuto daga Chedi, Karamar Hukumar Dawakin-Tofa, Kano. [email protected]

Amir Abdulazeez Twitter: @AmirAbdulazeez Facebook: https://m.facebook.com/amir.abdulazeez
2347080369796