Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan gyaran hanyar dan-ga-da da sauran matsalolin da suka dabaibaye tsohon ynkin karamar Hukumar Dawakin Tofa. Gwamnatin Jihar Kano a madadin al’ummar tsohuwar Dawakin Tofa. Al’ummar Tsohuwar Dawakin Tofa wadanda suka hadar da kananan hukumomin bagwai da Dawakin Tofa (Garin Gwamna), Tofa da Rimin gado. Hakika a wannan gwamnati mun fi kowa bada gudunwamar kafuwarta, kasancewar gwamnan dan yankin mu ne. To, amma a zahirin gaskiya wannan yanki, har yanzu ba mu gani a kasa ba. Mun zuba ido a wadannan ragowar kwanki da suka rage.
A fili take cewa duk Jihar Kano babu inda ya kaimu hanyoyi marasa kyau, matsalar ruwan sha da sauran matsaloli. hanyar bagwai zuwa ‘Dan-ga-’Da, guda ce daga cikin hanyoyi masu muhimmanci a wannan yanki, wato hanyar da tatashi daga Bagwai zuwa ‘Dan-ga-’Da, ta wuce Garo ta hade da titin Gwarzo. Mutanen wannan yanki suna shan wahala kwarai da gaske wajen zuwa asibiti da fito da kayan gonarsu. Hakika wannan yanki na tsohuwar Dawakin Tofa yana bukatar ayyuka da za su gamsar da jama’a su sake zabar gwamnatin a karo na biyu.
Daga Shu’aibu Adam bagwai. 07066420260 SHU’AIBU ADAM BAGWAI [email protected]