Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ta yi Allah wadai da kisan Shehun malamin Goni Aisami wanda wani soja ya yi a ranar Juma’a.
Matsayin Majalisar na dauke ne a wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun Mataimakin Sakatarenta, Farfesa Salisu Shehu.
- Matar mai wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ta ba da kodarta an dasa masa
- Gwamnati za ta ba da kwangilar tsaron Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
Majalisar ta yi kira da a gaggauta hukunta wadanda ake zargi, Adamu Gideon da Kuma John Gabriel.
Majalisar ta bukaci hukumar soji da ta shari’a da su yi biciken kwakwaf don gurfanar tare da hukunta wadanda aka kama da laifin kisan Sheikh Goni Aisami.
Sannan ta yi kira ga Musulmi da kada su kalli wannan kisa ta fuskar addinin, ballantana su yi kokarin daukar matakin da bai dace ba, kamar yadda wasu suke yi.
“Mu ba kamar su ba ne, mun yi imani daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” a cewar sanarwar.
Daga karshe sanarwar ta yi kira ga Musulmi da su kwantar da hankalinsu tare da barin doka ta yi aikinta.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi shi ne shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya.