✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A gaggauta bude titin Lokoja da direbobin tanka suka rufe —Gwamnan Kogi

Yahaya Bello ya ba da umarnin ne ta hannun mai ba shi shawara kan sha'anin tsaro, Jerry Omodara.

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bada umarnin bude hanyar Lokojo zuwa Abuja cikin gaggawa bayan direbobin tanka sun rufe ta a zanga-zangar da suke yi kan mutuwar mambansu.

Gwamnan ya ba da umarnin ne ranar Talata ta hannun mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro, Jerry Omodara a Lokoja.

Masu zanga-zangar dai sun rufe hanyar ce a daren ranar Litinin bayan daya daga cikin mambobinsu ya rasa ransa, sakamakon tsere wa sojoji da ya yi a shingen binciken Jamata bayan sun tsayar da shi, in da ya fada wani katon rami a daji.

Gwamnan ya bayyana damuwarsa bisa faruwar lamarin, sai dai ya yi Allah wadai da matakin da kungiyar ta dauka, inda ya shawarce su da su lalubo wata hanyar nuna bacin ran nasu.

Gwamnan Bello ya ce titin Lokoja zuwa Abuja hanyar zirga-zirga ce da ke da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya, don haka a cewarsa toshe ta zai durkusar da sana’o’i da rayukan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya ce: “Rufe hanyar da mutane ke amfani da ita ya saba wa dokar kasa, sannan ya taba sana’o’in mutane, ga masu bukatun da za su iya bukatar agajin gaggawa, misali mai juna biyun da ta fara nakuda”, in ji gwamnan.

Sai dai duk da hakan, Yahaya Bello, ya shawarci jami’an tsaro da su yi taka-tsantsan domin gudun tayar da hatsaniyar da za ta shafi zaman lafiyar kasar nan.

%d bloggers like this: