Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmi su fara duban watan Sallah daga ranar Asabar.
Daraktan Gudanarwa na NSCIA, Arc Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ne bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin majalisar ranar Juma’a.
- Shirye-shiryen Sallah: ’Yan kasuwar Kano na kokawa da karancin ciniki
- Sai an kula da hakkin marayu Najeriya za ta zauna lafiya — Sheikh Bala Lau
Ya ce biyo bayan shawarar da Kwamitin Ganin Wata na fadar ya bayar, Sarkin ya bukaci Musulman Najeriya da su fara neman jinjirin watan na Shawwal na shekarar 1443 bayan hijira wanda ya zo daidai da 30 ga watan Afrilun 2022, da zarar rana ta fadi.
Sanarwar ta ce, “Idan aka tabbatar da ganin watan daga adalan Musulmai, mai alfarma Sarkin Musulmi zai ayyana Lahadi, daya ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar daya ga watan Shawwal kuma ranar karamar Sallah.
“Amma idan ba a gan shi ba ranar Asabar din, ranar Litinin, biyu ga watan Mayu ce zata zama ranar Sallah.
“Kamar yadda aka saba yi a duk shekara bisa al’ada, shugabannin al’umma da malaman addinin Musulunci za a iya tuntuba don sanar da ganin watan,” inji Arc. Zubairu Haruna.
Sarkin ya kuma yi amfani da damar wajen tunatar da Musulmai kan wajabcin bayar da Zakkar Kono (Zakatul Fitri) ga masu karamin karfi a cikin al’umma.
Ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar ba wai kawai sun yi amfani da sanarwar kawai ba, amma su sanar da fadar a kan lokaci.
Al’ummar Musulmai dai a duk fadin duniya kan yi bikin karamar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan da suke shafe tsawon wata daya suna ibadar.