✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina kwatanta ayyukana da na sauran gwamnoni —Zulum

Gaskiya ba na jin dadi a duk lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna.

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya yaba wa dimbin masu yayatawa da kuma tallata ayyukansa a zaurukan sada zumunta.

Sai dai kuma gwamnan ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina kan abin da ya ce kowace jiha ta bambanta da takwararta.

Zulum ya yi wannan roko ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar ranar Litinin.

Gwamnan ya yaba wa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci.

“Duk da yake ina matukar godiya bisa dukkan goyon baya da tallata ayyukana, a kwanakin bayan nan, na samu sakonni, inda ake kwatanta ayyukan da muke yi a Borno da na wasu jihohi, a wasu lokutan ma har da cin mutunci.

“Gaskiya ba na jin dadi a duk lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan wadanda suke yin hakan suna cikin masu amfani da shafukan sada zumuntar da ke da alaka da mu”, in ji Gwamna Zulum.

“Ina daukar irin wannan kwatance da ake yi ba abu ba ne mai kyau, bugu da kari kuma ba gasa muke yi a tsakaninmu ba.

“Abin la’akari shi ne dukkan jihohi 36 na Najeriya suna da abubuwan da suka kebanta da su wajen bayar da muhimmanci, sannan akwai abubuwa da kowacce jiha ta fi la’akari da shi ta fuskar tsare-tsare na ci gaba da kuma bukatar al’umma.”

Dangane da Jihar Bornon, Zulum ya ce ya zama tilas su jajirce wajen sake farfado da ita duba da yadda ta samu koma baya a sanadiyar yakin da ta fuskanta na tsawo shekaru 12, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane ya kuma raba mutum miliyan biyu da matsugunansu da a yanzu suna bukatar agaji.