Akalla mutum tara ne cikin kowadanne ’yan Najeriya 10 ba sa isa cin lafiyayyen abinci, saboda ya fi karfinsu.
Wata babbar mai masana’anta, Misis Remi Kuteyi, ce ta sanar da haka, tana mai kira ga gwamnati ta da dauki matakan da suka dace domin samar da ingantacce kuma wadataccen yanayin da zai kai ga samar da lafiyayyen abinci mai dorewa a Najeriya.
- Rashin tsaro: Mutanen Tsafe sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua
- Gwamnati ta binciki kamfanonin da suke yin takin NPK –Sarkin Noman Bassa
Misis Kuteyi, wadda ita ce shugabar kamfanin masana’antun Spectra Industries Limited, ta bayyana haka ne a lokacin taron Ranar Abinci ta Duniya ta bana da kamfanin ya shirya a Legas.
A cewarta samuwar ingantaccen tsarin samar da abinci zai kawar da tasirin matsalolin tattalin arziki da na tabarbarewar sha’anin tsaro.
Don haka ta yi kira da a hada karfi da karfe domin samar da yanayin da zai kawar da matsalar rashin abinci mai gina jiki a Najeriya.
A cewarta, kamfanin ya shirya taron ne da nufin wayar da kan jama’a kan muhimmancin cin lafiyayyen abinci.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan Kamfanin, Mista Duro Kuteyi, ya ce an ware Ranar Abinci ta Duniya ne domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin cin lafiyayyen abinci domin samun koshin lafiya.
Don haka ya yi kira ga gwamanti da ta samar wa manoma ingatattun iri da maganin kwari da takin zamani, ta yadda hakan zai saukaka wa masu masana’antu kayan da suke bukata domin sarrafawa.
Sai dai ya koka da cewa faduwar darajar Naira na ci gaba da zama matsala ga masu masana’antu ta yadda ba kasafai suke iya samar da kaya a kan farashi mai rahusa ba.