Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biyan diyya ga al’ummar jiragen soji suka kai wa hari a lokacin da suke fatattakar ’yan ta’addan Lakurawa a yankin Ƙaramar Hukumar Silame da ke Jihar Sakkwato.
Jam’iyyar ta yi kiran ne a sako ta na ta’aziyya kan fararen hula suka jikkata da waɗanda suka gamu da ajalinsu a harin jiragen sojin a yankunan Gidan Sama da Rumtuwa da ke karamar hukumar.
Kakakin jam’iyyar ba kasa, Debo Ologunagba, a sanarwar da ya fitar kan harin kuskuren, ya buƙaci a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin tabbatar da amincin ’yan Najeriya da kuma kauce wa aukuwar hakan a nan gaba a yayin yaƙi da ’yan ta’adda.”
PDP ta jaddada goyon bayanta ga taki da ta’addanci, amma ta nuna muhimmancin kula da rayukan fararen hula.
- Sojojin Faransa: Dalilin da Janar Tchiani ya zargi Najeriya
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Suka Jure Wa Matsin 2024
“Irin haka ta faru a shekarar 2023 inda harin jiragen soji ya kashe fararen hula a Jihar Kaduna, ga shi kuma hakan ya maimaita kansa a 2024, don haka wajibi ne a ɗauki matakin hana ci-gabansa.
“Muna kira da a bayar da cikakkiyar diyyar waɗanda suka rasu tare da cikakkiyar kulawa da lafiyar waɗanda suka jikkata,” in ji sanarwar.
Duk da a kaka jam’iyyar ta buƙaci sojoji su ci gaba da ragargazar ’yan ta’adda domin muttsuke su a Najeriya.