Shugaba Muhammadu Buhari, ya umarci jami’an tsaro da su binciko kisan da aka yi wa sarkin Obudi-Agwa, Eze Ignitus Asor tare da wasu fadawansa a fadarsa da ke yankin Karamar Hukumar Oguta ta Jihar Imo.
A ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki fadar sarkin gargajiyar ana tsaka da zaman fada, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi ajalin sarkin da wasu daga cikin fadawansa.
- ’Yan takarar Gwamnan Gombe a kan sikeli
- Ya zargi Asibitin ATBUTH da yi masa kora da hali kan jinyar karayar dansa
Shugaba Buhari, yayin da yake mayar da martani kan lamarin a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya bukaci a gurfanar da wadanda suka aikata laifin domin su fuskanci shari’a.
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan, inda kuma jajanta wa iyalan wadanda suka mutu da sauran al’ummar yankin.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Eze Ignitus Asor, basaraken al’ummar Obudi-Agwa a Karamar Hukumar Oguta ta Jihar Imo.
“Shugaban kasa ya umarci hukumomin tsaro a jihar da su binciki wannan muguwar dabi’a tare da tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin sun fuskanci fushin doka.
“Yayin da yake jajantawa ‘yan uwa, abokan arziki da al’ummar Obudi-Agwa, da kuma duk wadanda harin ya shafa, shugaban ya yi addu’ar Ubangiji ya jikan wadanda suka mutu da bai wa wadanda suka jikkata sauki.
“Shugaba Buhari ya yaba da irin kokarin da gwamnatin Jihar Imo ke yi na inganta harkar tsaro, ya kuma bukaci daukacin al’ummar Imo da ‘yan kasar nan da su bayar da goyon baya ga kokarin hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki na jihar da sauran al’ummar yankin domin bai wa kowa kariya.”