Kasa da mako guda da yin aurenta, fitacciyar matashiyar nan mai rajin kare hakkin ’ya’ya mata ’yar kasar Pakistan, Malala Yousafzai, ta bayyana cewa a baya ta yi wa aure mummunar fahimta.
A wata hira da Mujallar Vogue ta yi da ita a shekarun baya, Malala ta bayyana rashin goyon bayanta ga yin aure, inda take cewa har ya zuwa lokacin, ta kasa gane dalilin da ya sa mutane ke yin aure, kamar yadda BBC ya ruwaito.
- Gwamnatin Kano ta dauki manoma 16,000 a shirin tallafin noma
- Budurwar da ta jira saurayinta shekara 16 ya fito a gidan yari
Sai dai a makon da ya gabata ne rahoton auren Malala da angonta Asser Mlik ya bulla cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
A cikin sakon, Malala ta wallafa yadda aka gudanar da kwarya-kwaryar bikin murnar auren a gidansu da ke garin Birmingham a Birtaniya.
Bayan mako guda da bikin ne ta yi hira da BBC, inda ta bayyana cewa a baya ta yi wa auren mummunar fahimta, amma a halin yanzu ta samu miji kuma abokin rayuwa.
Ta bayyana cewa dama ita ba wai adawa take da auren ba, kawai al’adun cikin auren ne suka ci karo da akidunta na fafutukar kare hakkin mata.
Kasa da mako guda da yin aurenta, fitacciyar mai fafutikar kan ilimin ’ya’ya mata kuma wadda ta samu kyautar Nobel ta zaman lafiya, Malala Yousafzai, ta bayyana cewa a baya ta yi wa aure mummunar fahimta.
A hirar da shirin Andrew Marr na BBC, matashiyar mai shekara 24, ta ce da gaske ne ta damu matuka, a kan halin da ’yan mata ke fuskanta a sassa daban-daban na duniya saboda auren wuri.
Mai gabatar da shirin ya fara ne da taya Malala murnar auren da ta yi a makon da ya wuce, daga nan ya jefo mata tambayar abin da ya sauya tunaninta a kan aure, alhalin a baya tana adawa da shi?
Sai Malala ta kada baki ta ce: “Ba na adawa da aure, na dai damu ne da yadda ake yin auren da abin da yara mata masu kananan shekaru da aka yi wa suke fuskanta, da auren dole, da halin da suke shiga bayan mutuwar auren, da kuma rashin daidaito tsakanin miji da mata, su ne abubuwan da ke matukar daga min hankali.