Gwamnatin Tarayya ta ce nan da watanni 14 za a kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya sanar da haka a yayin ƙaddamar da aikin rukunin farko na aikin daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Alhamis.
Rukunin farko na aikin ya tashi nema daga Abuja zuwa Kaduna, kashi na biyu kuma Kaduna zuwa Zariya, sai kashi na uku daga Zariya zuwa Kano.
Ministan ya ce Ministan Ayyuka David Umahi ya bayyana cewa an kawo ƙarshen siyasar aikin gyaran titin, kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba zai lamunci jan ƙafar aikin ba.
Ya ce, “shi ya sa aka karɓe aikin daga kamfanin Julius Berger saboda suna so sai shekara uku za su kammala, amma muka ce a wata 14 muke so.
“Wannan ya sa aka raba aikin aka ba wa kamfanoni uku domin sauƙaƙa aikin. Saboda ’yan Najeriya sun ƙosa kammala aikin.
“Shugaban Ƙasa ya ba da umarni kuma Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ba da haɗin kan da ake buƙata don haka na za a samu matsala ba.
“Nan da wata 14 za mu fara aiki da sabon titi daga Abuja zuwa Kano,” in ji Ministan.
A nasa ɓangaren, Umahi ya bayyana cewa za a tsawaita aikin da kilomita biyar zuwa Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, da kuma wani kilomita biyar ta ɓangaren Abuja zuwa Lakwaja.