✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa sun harbe direba, sun sace uwa da danta a Nasarawa

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Litinin a Karamar Hukumar Toto da ke Jihar.

’Yan bindiga sun harbe wani direban mota sannan suka yi garkuwa da wata uwa tare da yaronta mai shekara uku a duniya.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Litinin a hanyar Ugya zuwa Umaisha a Karamar Hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa.

  1. Rashin tsaro: Aisha Buhari ta bukaci daukar karin jami’an tsaro
  2. Ana mini barazanar kisa kan yaki da cin hanci —Shugaban EFCC

Da yake bayani daga gadon asibiti, direban mai suna Abdullahi Abubakar ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:45 na yammacin ranar ta Litinin.

A cewarsa, “Lokacin da muka yi arba da su, sai suka bude wa motarmu wuta, nan take na gaza rike motar muka yi cikin daji, a nan ne suka zo suka yi awon gaba da su.”

Ya ce ’yan bindigar da adadinsu zai kai kusan 20 sun bude wa motarsa wuta inda harsashi ya gogi gefen kansa, wanda a dalilin haka ya kasa rike motar.

Ya kara da cewar daga bisani sun rabu da shi bayan da suka yi tsammanin ya mutu.

Wani direba da ya tsallake rijiya da baya a sanadin harin, Zakari Musa ya ce shima sun bude masa wuta tare da fasa masa gilashin motarsa.

Ya ce yana dauke da wani soja tare da wasu fasinjoji yayin da suka yi kacibus da ’yan bindigar, nan take suka bude wuta kuma harsashi ya sami sojan a wuya.

“Allah ne kadai ya kare mu saboda sun harbi motata daga baya har suka fasa min gilashi,” a cewarsa.

Shugaban Sashen Watsa Labarai na Karamar Hukumar Toto, Mista Hagai Daniel ya tabbatar wa da wakilinmu faruwar harin ta wayar tarho.

Ya ce ko a makon da ya gabata sai da suka yi taro kan sha’anin tsaron da ya shafi Karamar Hukumar, da nufin lalubo bakin zaren matsalar.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel bai daga wayar da wakilinmu ya buga masa ba bare a ji ta bakinsa kan harin.