Yan adawa sun gudanar da zanga-zangar lumana a Accra babban birnin kasar Ghana don nuna kyamarsu kan matsi da tsadar rayuwa a mulkin Shugaban Kasar, Nana Akufo-Addo.
Zanga-zangar dai ta sami halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na kasar, dauke da kwalaye masu rubutun neman sassauki kan irin matsin rayuwar da suke fuskanta.
- Bidiyon Dala: Kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar N800,000
- Cutar Shan-inna ta sake bulla a Jihohi 13 da Abuja
Wannan dai shine karo na farko da babbar jam’iyyar adawa ta NDC ta shirya irin wannan zanga-zangar tun bayan watan Maris, 2021 lokacin da kotun koli tayi watsi da kalubalantar sakamakon zaben Shugaban Kasar da aka yi wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Akufo-Addo.
Shugaban dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga ’yan adawa da gwamnatinsa, saboda matsalar tattalin arziki da kasar ta fada a sanadiyyar annobar COVID-19.
To sai dai wasu daga cikin masu zanga-zangar biyu sun mutu a yankin Ashanti a watan jiya lokacin da suke korafi kan mutuwar wani matashi mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Ibrahim ‘Kaaka’ Mohammed.
Gwamnatin kasar dai ta fito da sabon haraji kan jama’ar kasar da kuma kara farashin man fetur domin kara samun kudaden shiga, sakamakon bashin da ake bin ta da kuma raguwar kudaden da take samu, a dalilin barkewar annonar Coronavirus.