Duk da kasancewarta matashiya, Barista Rabi Adamu Musa-Manchi kwararriyar lauya ce kuma ’yar siyasa. Tana daya daga cikin matasan da aka gayyata Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayin sanya wa dokar ba matasa damar tsayawa takara (Not Too Young to Run). Aminiya ta zanta da ita inda ta yi bayani a kan rayuwarta da ayyukanta da kuma muhimmancin barin mata su shiga siyasa don bayar da gudummawarsu wajen ayyukan ci gaban kasa:
Tarihina a takaice:
Sunana Barista Rabi Adamu Musa-Manchi. An haife ni a Ungwar Maigizo a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna a 1985. Yanzu ina da shekara 34 ke nan.
Na yi karatu ne a makarantar firamare ta Baptist Nursery & Primary School da ke garin Kafanchan. Daga nan na koma Makarantar Ma’aikatan Kwalejin Ilimi (College of Education Staff School), Kafanchan inda na kammala firamare. Bayan nan sai na shiga sakandare a Kaduna Capital School da ke Ungwar Malali a Kaduna. Bayan na gama sai na samu shiga Jami’ar Jos da ke Jihar Filato inda na karanta aikin lauya (Cibil Law). Bayan kammala digiri a kan aikin lauya sai na tafi makarantar horar da lauyoyi da ke Kano (Nigerian Law School), inda na samu shaidar zama barista inda na zama cikakkiyar lauya a watan Nuwamban 2012.
Na yi wa kasa hidima (NYSC) a garin Abuja a shekarar 2012 zuwa 2013.
Sai dai kafin a kira ni don tabbatar min da wannan matsayi, na yi amfani da wannan damar zuwa wata jami’a a kasar Amurka wacce ake kira Unibersity of Connecticut (Ucon) inda na yi kwas a kan gudanar da harkokin rayuwa (Social Entrepreneurship).
A shekarar 2013 an zabe ni na zama wakiliya a taron matasa na Youth Assembly a watan Janairun 2013 a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ta kasar Amurka.
Na yi kwasa-kwasai da dama da na mallaki satifiket. Daga ciki akwai satifiket da na mallaka kan ilimin Kwamfuta da na Sauyin Yanayi (Climate Change). Akwai su da yawa dai gaskiya.
Aikace-aikacen da na yi:
Na yi aiki da Riders for Help, wata kungiyar sufuri ce ta kasar Birtaniya. Sannan a lokacin da nake daliba a jami’a na yi aiki da wata kungiya mai suna Africa Youth Platform for Debelopment, ita ma kamar waccan, kungiya ce mai zaman kanta wacce na zama kodinetanta a Jihar Filato.
Sannan zuwa yanzu na bude gidan wasan yara mai suna Taurus Kid a garin Kafanchan wanda shi ne irinsa na farko a Kudancin Kaduna.
A yanzu haka ina aikin lauya inda nake zaune a Abuja.
Burina lokacin da nake karama:
Burina ina karama shi ne in zama lauya. A duk lokacin da aka tambaye ni me nake son zama idan na girma ba ni da wata amsa face in zama lauya. Ba zan manta ba tun ina makarantar firamare burina ke nan kuma ga shi Allah Ya tabbatar min da burina. Bayan na kammala karamar sakandare na shiga babbar sakandare sai na dauki darussan fasaha ‘Art’ sai mahaifina ya zo ya samu shugaban makarantar a lokacin ana kiransa Malam Dodo ya ce masa shi yana so ’yarsa ta karanci darussan kimiyya (Science) domin duk ’ya’yansa abin da suka karanta ke nan ni kuma na ce atafau darussan fasaha nake so. Ya ce me ya sa nake son bangaren, na ce saboda ina so in zama lauya wanda burina ba zai cika ba idan na karanta darussan kimiyya. Mahaifina ya yi min fada sosai a ofishin shugaban makarantar har ma mataimakin shugaban yake ce masa tunda abin da yarinyar take so ta zama ke nan to a bar ta ta yi darussan da take so. Ran mahafina a lokacin gaskiya ya baci amma ga shi yanzu yana farin ciki da zamowata lauya.
Bayan na ci jarrabawar WAEC da NECO sai na fara da yin Difiloma a fannin lauya kafin in je in yi digiri dina. Bayan shekara kamar biyu da zamata lauya sai muka hadu da mataimakin shugaban makarantar sakandaren da na gama. Bayan mun gaisa na ce masa ko ya tuna da ni? Ya ce e amma dai ba sosai ba, sai na ce masa ko zai tuna lokaci kaza da aka yi magana a kan kaza? To ga shi yanzu har na zama lauya burina ya cika sai muka yi dariya. Na gode Allah da cikar wannan buri.
Wuraren da na ziyarta:
Na ziyarci kasashe da dama. Bari mu fara da kasar Amurka inda na je manyan garuruwan da suka hada da Georgia da Atlanta da Massachuset. Na je Washinton DC inda na ziyarci har Fadar White House. Na je Thomas Jefferson Memorial. Na je dandalin ’yanci a New York da cibiyar fina-finan Hollywood a California da Philadelphia da ke Jihar Pennsylbania sannan na je Chicago da wurare da yawa a kasar Amurka.
Bayan kasar Amurka na je birnin Paris da ke kasar Faransa sannan na je kasar Jamus wani gari da ke Jihar Hamburg da wasu garuruwa wadanda ba zan iya kawowa ba saboda sunayen nasu da yarensu ne suna da wahalar fada. Sai kuma wani gari guda daya da na je a kasar Ingila wanda yake birnin Landan.
Gaskiya tafiye-tafiye shi ne babban abin da yake debe min kewa a rayuwa don ina matukar sha’awar tafiye-tafiye. Yawancin tafiye-tafiyen na yi su ne don kwasa-kwasai sai wasu kadan da na je don ziyara.
A cikin gida Najeriya kuwa na je Gombe sai kuma Jihar Filato inda nan kuma shi ne garina na biyu don mahaifiyata ’yar Jos ce kuma nakan je har yanzu duk da mahaifiyata ta rasu amma kakata tana nan da ranta a Jos. Na je Legas da Bauchi da Nasarawa da Kogi. Yankin Kudu maso Gabas ne kawai ban taba zuwa ba.
Kungiyoyin da nake ciki:
Akwai kungiyoyi musamman masu zaman kansu na gida da na waje wadanda na yi aiki da su da wadanda nake aiki da su kamar, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) da Kungiyar Yaki da Musguna wa Mata ta Women Against Biolence Initiatibe, wacce ni mamba ce. Sannan ni mamba ce a Kungiyar Tsofaffin Daliban Musaya ta Amurka (United State Edchange Alumni) da Kungiyar Matasa Mata ’Yan siyasa (Nigerian Young Women in Politics Forum). Har ila yau ni mamba ce a Jam’iyyar APC da kuma bangaren mata matasa na Jam’iyyar APC mai suna Young Women Forum.
Har ila yau ni mamba ce a kungiyar Not Too Young to Run inda har aka ba ni dama na kasance cikin wadanda suka halarci Fadar Shugaban Kasa a lokacin sanya wa dokar hannu da ya yi a bara don bai wa matasa damar fafatawa a harkokin siyasar kasar nan.
Abin da ya sa na shiga siyasa:
Siyasa dai na dade ina yinta tun ina makaranta domin mun yi siyasa ta kungiyar dalibai ta jami’a da kuma kungiyar daliban da ke koyon aikin lauya (Law Students Society) inda har na taba fitowa takarar Ma’aji. Duk lokacin da na dauka a jami’a ina cikin harkokin siyasar kungiya a lokacin ina cike da burin cewa wata rana zan kasance cikin harkokin siyasa gadan-gadan.
Amma abin da ya janyo ra’ayina a kwanan nan don shiga siyasar Najeriya shi ne burin da nake da shi na ganin ana damawa da matasa musamman mata da aka bar su a baya. Na lura ba ma a kasar nan ba a duniyar ma gaba daya an bar mata a baya a fannin siyasa domin duk daukar da wadansu ke yi cewa da an ce ke ’yar siyasa ce kina ’ya mace sai su fara tunanin ke ’yar iska ce ana miki kallon mutuniyar banza. Wannan ya sa na ce bari mu shigo ciki don nuna wa mutane cewa ba haka harkar take ba. Ina son wayar da kan jama’a su daina tunanin haka. A daina yi wa mata kallon mutanen banza don suna siyasa. Misali ni ai matar aure ce kuma ina da ’ya da maigida wanda shi ne ma ya karfafa min gwiwa da in shiga siyasa dari bisa dari. Ina so a rika damawa da mata da kuma matasa a harkokin mulki a kasar nan. Ina ganin akwai matsalar rashin shigar mata cikin siyasa saboda mata su ne suke da tausayi don haka mu ya kamata mu taimaka wa jama’a wajen fid da su daga halin da suke ciki.
Ina son samun damar kirkiro dokoki da za su rika taimaka wa jama’a musamman wajen kawar da fatara da talauci da rashin aikin yi.
Wacce nake koyi da ita a rayuwa:
Allah Ya jikan mahaifiyata Malama Misis Chundum Adamu Musa. Gaskiya ita ce abin koyina ta farko a rayuwa saboda yadda take matukar kaunar zaman lafiya a cikin iyali da kuma cikin al’umma sannan da sauran abubuwa da dama. Bayan ita ina da ’yan uwa mata biyu wadanda su ma ina matukar koyi da salon rayuwarsu. Bayan na cikin gida kuma ina da wadansu daban a waje da nake koyi da su da suka hada da Misis Cecelia Musa wacce ta fito takarar shugabancin Karamar Hukumar Jama’a kafin abin da ya faru dai ya faru. Gaskiya ita mace ce kamar maza mai kokarin son taimaka wa al’umma wacce har yanzu nakan nemi shawararta a siyasa. Bayan ita kuma akwai wata tsohuwar ma’aikaciyar gidan talabijin na kasa (NTA) wanda yanzu mataimakiya ce ta musamman ga Shugaban Kasa kan ’yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, wato Abike Dabiri-Erewa. Bayan ita akwai Hajiya Hafsat Baba, Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Kaduna.
Lokacin da na hadu da maigidana:
To asali dai mun yi makaranta daya da shi duk da cewa yana gaba da ni kafin kowa ya kama gabansa. Duk da cewa asalinmu duka daga Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna muke. Shi ya fito ne daga Gundumar Barde ni kuma daga Gundumar Maigizo amma mun sake haduwa da shi ne wata rana na je yin fasfo a ofishin jami’an kula da shige da fice a Abuja shi kuma a lokacin jami’in shigi da fice ne, to a nan ne dmuka fara kulla soyayya da shi bayan ya bijiro da bukatarsa na sona ni ma sai na amince kawai shi ke nan kan a je ko’ina sai maganar aure. A yanzu muna da ’ya mace guda daya da shi. Muna zaman lafiya da juna kuma muna zaune a Abuja ni ina aikina na lauya shi kuma yana aikinsa.
Kaya da kuma launin da na fi so:
A gaskiya ni ba ’yar kwalisa ba ce. Duk wani kaya mai mutunci da ya dace da ni shi nake sakawa. Amma na fi son riga da dogon siket. Bana yin fente-fenten fuska sai dai shafa hoda kadan haka amma dai ba na son kazanta a rayuwata. Launin da na fi so kuma shi ne kore. Ina son korran abubuwa abin da ya sa ma duk lokacin da na tashi da safe sai na fito na kalli furannin da ke farfajiyar gidana duk da dai kayanmu na lauyoyi fari da baki ne, amma dai kore nafi so.
Abincin da na fi so:
Doya shi ne babban abincin da na fi so a rayuwata musamman da miyar jajjage haka da za a hada da kifi ko naman kaza. Koda na je Amurka sai da na nemi inda ake sayar da doya na saya duk da tsadarsa ga shi yanzu ’yata ta gaji son cin naman kaza.
Shawarata ga iyaye mata:
Ina bai wa iyaye mata da su daina sakaci da karatun ’ya’yansu musamman mata. Ni ba na kaunar ganin yara mata na yawon tallace-tallace. Haka ma idan ’ya’ya mata sun nuna sha’awarsu da son shiga harkar siyasa ya kamata a rika barinsu suna yi illa iyaka a rika nuna musu abin da ya dace da wanda bai dace ba, domin in har ba mu bari wadanda muka ba su tarbiyya sun shiga ba, to marasa tarbiyya sai su mamaye, tunda dole ne dai a dama da mata ko muna so ko ba ma so. Sannan mata su tashi tsaye wajen neman abin hannunsu don rufa wa juna asiri su da mazansu.