✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2027: Tsohon IGP ya fito takarar gwamna, ƙungiya ta mara masa baya a Nasarawa 

Adamu ya yi alƙawarin kafa gwamnati mai sauraron jama’a da kula da buƙatunsu idan har aka zaɓe shi ya zama gwamnan jihar.

Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki.

“Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar.

Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen.

AGNP ta yaba wa Adamu bisa sauye-sauyen da ya kawo a lokacin da yake Sufeto Janar na ’Yan Sanda, musamman wajen samar da tsarin ‘yan sanda a cikin al’umma, amfani da leƙen asiri wajen yaƙar laifi da kuma fasahar zamani.

Ƙungiyar ta ce hakan na nuna irin cancantar da yake da ita wajen kawo ci gaba a Nasarawa.

“Waɗannan su ne irin manufofi masu amfani da jama’a ke buƙata a matakin jiha,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta samu sa hannun Daraktan ƙungiyar, Husseini Gana, da Sakataren Yaɗa Labarai, Saliu Hamzat.

Sun ce ƙungiyar ta yi nazari sosai kan masu neman takara kafin ta mara wa Adamu baya.

Sun kuma jaddada cewa Adamu ya taka rawar gani wajen hidimta wa jama’a, ayyukan jin-ƙai da kuma samar da ci gaba.

“Kodayake ba jam’iyya muke ba, amma muna da tabbacin cewa Mohammed Adamu shi ne ɗan takarar da ya fi cancanta ya gaji gwamnan yanzu,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta ce ta riga ta fara shirin samun goyon bayan jama’a daga ƙauyuka da birane, inda ta tabbatar da cewa za ta samar wa Adamu ƙuri’a sama da miliyan ɗaya a lokacin zaɓen.

AGNP ta kuma buƙaci jam’iyyar APC mai mulki da ta bai wa Adamu tikitin takarar gwamnan jihar a 2027.

“Jagoranci da mulki al’amura ne na haɗin gwiwar kowa da kowa,” in ji Hamzat.

“Muna da yaƙinin cewa tare da Mohammed Adamu, Nasarawa za ta ga sabon salon ci gaba da ya dace.”

Tun da farko, Adamu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Nasarawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, a lokacin wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Lafia, babban birnin jihar.

Ya ce matakin ya biyo bayan kiraye-kirayen jama’a waɗanda ke da yaƙinin cewa yana da ƙwarewa da gogewa a fannin mulki.

Adamu ya yi alƙawarin kafa gwamnati mai sauraron jama’a da kula da buƙatunsu idan har aka zaɓe shi ya zama gwamnan jihar.