✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Can ta matse wa ’yan Najeriya, dadina nake ji —Emefiele

Ya ce idan zuciyar ’yan Najeriya ta ga dama ta buga, shi hankalinsa a kwance yake

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya ce hankalinsa a kwance yake duk da yadda batun takararsa ya yamutsa hazo a Najeriya.

Emefiele ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin ’yan jarida bayan wata ganawar sirri da suka yi da Shugaba Buhari a Dadar Shugaban da ke Abuja.

Da aka tambayi Gwamnan na CBN kan umarnin da Buhari ya bayar cewa ya ajiye mukaminsa bayan sayen fom din takarar shugaban kasa, sai ya ce “Yansu dai babu wani wani labari kan hakan, eh kun ji da kyau, cewa na yi baba labari a kai tukuna, amma labari na nan tafe nan gaba kadan”

Da aka tambaye shi kan ra’ayoyin ’yan Najeriya game da takarar tasa, sai ya kada baki ya ce “Can ta matse musu, idan zuciyarsu ta ga dama ta buga, ni dai dadina nake ”.

Tun bayan lokacin da gwamnan na CBN ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa ’yan Najeriya ke ka-ce-na-ce kan ya ajiye mukaminsa.

Shi ma Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce takarar Emefiele, wuce gona da iri iri, sannan ya bukaci shugaban kasar ya kore shi idan ya ki ajiye mukaminsa.

A ranar Laraba ne dai Shugaba Buhari ya umarci duk masu rike da mukaman siyasa da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati da ke neman takara a zaben 2023 su ajiye aiki zuwa ranar Litinin 16 ga watan Mayu da muke ciki.

Sashe na 84 (12) na Dokar Zabe ta 2022 ta haramta da duk wani mai rike da mukamin siyasa shiga harkokin siyasa ko zabe, ba tare da ya sauka daga mukaminsa ba.

Ana ganin wannan doka ta shafi Emefiele da ministoci da jakadu da sauran  nadaddun shugabannnin hukumomi ma’aikatu.

Sai dai Gwamnan na CBN na kalubalantar hakan a kotu, ta hannun lauyansa, Mike Ozekhome (SAN), bisa hujjar ceya mukaminsa ba na siyasa ba ne.

A cewarsu, ranar 23 ga watan Fabrairun 2023, watan da za a yi zaben shugaban kasar ya kamata ya ajiye aiki.

%d bloggers like this: