Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce babu ruwanta da murdiyar zabe amma ’yan siyasa ne ke aikata hakan.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinar hukumar ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, yayin ganawarta da manema labarai da kungiyoyi a jihar.
- NAJERIYA A YAU: Karin Kudi: Akwai Yiwuwar Daliban Jami’ar Maiduguri Su Daina Karatu
- Na daina jin dadin rayuwa, burina in cika da imani kawai – Aminu Dantata
Ta ce, “INEC ba ta murdiyar zabe, ’yan siyasa ne ke aikata haka.”
Onyeka ta ce babu wata kafa da hukumar za ta bari wadda za ta ba da damar murdiyar zabe a 2023.
Ta kara da cewa, murde zabe a wannan karo abu ne mai wahalar gaske saboda kyakkyawan shirin da hukumar ta yi wa manyan zabukan 2023.
A cewarta, hukumar za ta yi iya yinta wajen tabbatar da sahihin zabe, kuma ba za ta bari kowane irin matsin lamba daga ko’ina ya yi tasiri a kanta ba.