✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: ’Yan kasuwa sun yi alkawarin saya wa Atiku fom din takara

Kungiyar dai ta ce ko nawa ne za ta sai masa fom din.

Hadaddiyyar Kungiyar ’Yan Kasuwan yankin Arewa maso Gabas masu goyon bayan Atiku Abubakar, sun yi alkawarin saya wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasar fom din takarar Shugaban Kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Jami’in kungiyar na shiyyar, Dokta Ali Adamu Bappayo, ne ya bayyana hakan a lokacin taron kaddamar da kungiyar da bikin bude ofishinta na shiyyar da ke Gombe ranar Alhamis.

Ya ce su a shirye ’yan kasuwar suke  su saya masa fom din takarar ko nawa ne muddin ya amince zai tsaya.

Dokta Ali Bappayo, ya ce sun kirkiro kungiyar ne saboda ganin halin da yankin yake ciki na fama da rashin tsaro ga yawan jama’a marasa aikin yi.

Da yake mayar da jawabi Alhaji Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa ya bayyana jin dadinsa da abin da ’yan kasuwar suka yi na alkawarin saya masa fom din.

Ya ce bai taba ganin irin halin kunci da aka shiga irin na wannan lokacin ba, inda ya ce ya fara siyasa tun a shekarar 1992, amma bai taba ganin kuncin rayuwa irin na wannan karon ba.

Ariku ya ce a kan haka, ya zama dole a tashi tsaye a yake shi, kuma shi zai gyara idan ya zama shugaban Najeriya.

“Na Yarda na amsa kiran ’yan kasuwa zan tsaya takara a 2023  kuma na gode da aniyarsu ta saya min fom din takara” inji Atiku.

 A nasa tsokacin tsohon Ministan ’Yan Sanda kuma tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Adamu Maina Waziri, ya ce Atiku ya cancanta ya shugabanci Najeriya don ya ceto kasar daga halin da take ciki.