✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Yadda za a fafata yakin neman kuri’un ’yan Najeriya miliyan 84

A takaice za a kashe fiye da Naira miliyan 500 wajen gudanar da gangami a kowace jiha.

A ranar Laraba ce aka bayar da damar fara yakin neman zabe kamar yadda jadawalin Hukumar INEC ya nuna.

Ana hasashen cewa manyan ’yan takara hudu na Shugaban Kasa, wato tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi za su kashe biliyoyin Naira domin yakin neman zaben da aka fara.

Jam’iyyun siyasa 18 ne suka tsayar da ’yan takara a zaben na Shugaban Kasa, wanda Hukumar INEC ta shirya gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairun badi.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan takarar tuni suka fara hada-hadar kudade gabanin ma a fara yakin neman zaben.

Za a kashe wadannan kudaden ne wajen kamfe a jihohi, shirya taruka, biyan tallacetallace da sauransu.

Duk wadannan ayyukan da sauransu, za a yi su ne domin neman kuri’un mutanen Najeriya.

Kididdigar Hukumar INEC ta nuna cewa akwai wadanda suka yi rajistar zabe a kasar su 84,004,089, wanda hakan ke nuna akwai akalla wadanda suka cancanci kada kuri’a mutum miliyan 84, duk da cewa ba dukansu ne suke yin zaben ba.

Haka kuma za a kashe wasu kudaden wajen jawo hankalin wasu mutane su zabi dan takara, a wani yanayi da ke ci wa dimokuradiyyar Najeriya tuwo a kwarya, wato sayan kuri’a.

Biliyoyin kudaden da za a kashe

Sashi na 88 (2) na Dokar Zabe ta 2022 ya bayyana adadin kudaden da dan takara zai kashe a zaben Shugaban Kasa a kan Naira biliyan 5, yayin da karamin sashe na (9) na wannan tanadin ya nuna cewa dan takarar da ya aikata da gangan ya saba wa wannan sashe ya aikata laifi kuma za a iya yanke masa hukunci na tarar kashi 1 cikin 100 na adadin da aka ba da izini a matsayin kudin yakin neman zabe a karkashin wannan dokar ko kuma dauri na wani lokaci, wanda bai wuce wata 12 ba, ko duka biyun.

Sai dai kuma manyan jiga-jigan jam’iyyu da ’yan kwamitin yakin neman zabe da ’yan siyasa da masana sun yi hasashen cewa kudaden da ake kashewa a yakin neman zabe na shekarar 2023 zai zarce na shekarar 2019, la’akari da hauhawar farashin kayayyaki. Idan ba a manta ba, a zaben shekarar 2019 kudin da doka ta amince a kashe a yakin neman zaben Shugaban Kasa, Naira biliyan daya ne.

Sai dai kuma bayan yi wa dokar zabe gyara aka kara shi zuwa Naira biliyan biyar.

An fara kamfe…

A ranar Laraba ce dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin neman zabensa bayan ya gabatar da wasu littattafai guda uku.

Kafin nan, a ranar Talata dan takarar na PDP ya kai ziyara Jihar Enugu domin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na yankin Kudu maso Gabas.

Sai dai taron ya bar baya da kura, inda Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu da Sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Sanata Chimaroke Nnamani da sauransu suka kaurace wa taron.

Shi dai Ikpeazu yana cikin wadanda suke tare da Gwamna Wike na Jihar Ribas, wadanda suka bayyana cewa ba za su shiga yakin neman zaben na Atiku ba, har sai an biya musu bukatunsu, ciki kuwa har da saukar Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Dokta Ayu.

Sai dai Kwamishinan Kasuwanci da Hannayen Jari na jihar, Cif John Kalu ya ce Gwamnan Abia din bai samu halartar taron ba ne saboda bai dade daga dawowa daga tafiya daga wata kasa ba.

Haka kuma a ranar kaddamar da yakin neman zaben bayan kaddamar da littafan, Aminiya ta lura wasu gwamnonin PDP da sauran wadanda suke bangaren Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike, ba su halarci taron ba.

Gwamnonin da ba su zo su ne: Samuel Ortom na Jihar Binuwei da Seyi Makinde na Jihar Oyu da Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da Okezie Ikpeazu na Jihar Abia da sauransu.

Ana sa rana ’yan takara za su ziyarci kowace jiha daga cikin jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), domin tallata kansu.

Wani jigo a jam’iyya mai mulki da ya halarci yakin neman zaben Shugaban Kasa har sau uku, ya ce kudaden da ake kashewa wajen gangamin sun hada da hayar jiragen sama, daukar hayar wuraren gudanar da taro, ababen hawa, tara magoya baya zuwa wurin gudanar da taro da kai ziyara ga sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a lokacin.

“A takaice za a kashe fiye da Naira miliyan 500 wajen gudanar da gangami a kowace jiha.

“Domin kuna so ku tsoratar da abokin adawar ku, za ku iya hayar mutane daga jihohin da ke makwabtaka da ku domin ku samu jama’ar da ake so,” inji shi.

APC ta dage kaddamar da yakin neman zabenta

A daya bangaren kuma, Jam’iyyar APC ta dage kaddamar da fara yakin neman zabenta, wanda a da shi ma aka shirya yi a shekaranjiya Laraba.

Daraktan Kamfe na jam’iyyar, Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ne ya sanar da hakan, inda ya ce an yi haka ne, domin a samu damar fadada kwamitin tare da sanya wasu mutanen da babu su a ciki kwamitin da farko, domin tafiya da kowa.

Mako mai zuwa za mu fara kamfe – NNPP

A nata bangaren, Jam’iyyar NNPP ta ce sai mako mai zuwa za ta kaddamar da kamfe, inda ta ce ta yi haka domin kara shiri. Daraktan Yada Labarai na jam’iyyar, Dokta Agbor Major ya ce suna shirin fara kamfe din ne a yankin Arewa ta Tsakiya daga makon gobe.

Muna ci gaba da tattaunawa – LP

Ita kuma Jam’iyyar Labour Party ta ce har yanzu tana ci gaba da tattaunawa ne da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, domin fitar da kwamitin yakin neman zaben.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Kwamrade Arabambi Abayomi ne ya bayyana hakan, inda ya ce jam’iyyarsu ta zama wadda aka fi shauki a cikin jam’iyyu, shi ya sa suke dan kafa domin fitar da kwamitin nagartattun mutane.

Tallata dan takara

Shi kansa wannan bangare na lamushe makudan kudade, domin muhimmancin da hakan yake da shi ga ’yan takara.

Bangaren tallata dan takara ya hada da yin riguna, huluna, buga hotuna, kai tallace-tallace kafafen watsa labarai, mawaka, daukar nauyin tattaunawa da sauransu, wanda a hakan akan iya ware misalin Naira biliyan 2.

Sai dai wani mamba a kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya ce “Siyasa dabara ce, domin idan kana sayar da kayanka kokari za ka yi ka tabbatar mutane sun gamsu da shi, har su saya.

“Muna da abin sayarwa kuma kayan sayarwarmu na kwarai, shi ne Bola Ahmed Tinubu, Jagaban. Don haka za mu sa shi kasuwa ga jama’a don su san ingancinsa kuma tabbas mun san za su saya.”

Shi ma wani jigo a Jam’iyyar PDP ya ce jam’iyyar tana da irin tsarin ta na yadda take gudanar da yakin neman zabenta da kuma abin da ya kunsa.

“Ba zan iya fada maka ainihin kudaden da za mu kashe ba amma ana bukatar biliyoyin Naira. Amma na fadi haka ne, don ina da yakinin cewar jam’iyyar da shi kansa Atiku a shirye suke kuma sun yi daidai da aikin.

“Shi (Atiku) yana tafiye-tafiye na kasuwanci zuwa Dubai da Turai, ka san shi dan kasuwa ne. Kuma na yi imani ya shirya tsaf don ci gaba da gudanar da yakin neman zaben da aka fara.

“Kalubalen da kawai muke fuskanta bai wuce matsalar da jam’iyyar ke ciki na rikici tsakanin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Iyorchia Ayu da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ba.”

Sai dai abu mafi girma, a cewar manyan jiga-jigan jam’iyyun, shi ne abin da ake kashewa a ranar zabe.

Kudaden dai, inji su, za a fara ne da harhada kodinetoci na jihohi.

Wani dan Jam’iyyar APC a yankin Arewa ya ce kashe Naira biliyan 5 ai abin dariya ne ga dimokuradiyya.

Yana mai cewa kudaden ko zaben gwamna ba za su iya gudanarwa ba, ko da a kananan jihohi irin su Bayelsa da Zamfara.

Ba mu san nawa APC da PDP suka kashe a zaben 2019 ba – INEC

A wani labarin daban, Hukumar INEC ta ce har yanzu Jam’iyyar APC da PDP da sauransu ba su kawo musu bayanin kudaden da suke kashe a zaben 2019 ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, inda ya ce daga cikin jam’iyyu 91 da suka shiga zaben, kusan 34 ne kawai suka kawo bayanan kashe kudadensu, wadanda suka kunshi kudaden da suka samu da wadanda suka kashe.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa daga cikin jam’iyyun da suka kai rahoton yadda suka kashe kudadensu, babu APC da PDP da sauransu.