Babban Daraktan kungiyar magoya bayan Yarima (YSO), Ambasada Bala Adamu, ya bayyana cewa wadanda suka yi ammana da Sanata Ahmed Sani Yarima ne suka bayar da gudumawa daga kan N100 zuwa N500,000, domin saya masa fom din neman takarar shugaban kasa kan kudi miliyan 100 a APC.
Ya bayyana haka ne ranar Juma’a a Abuja, yayin da yake mika fom din takarar ga Sanata Yarima domin ya tsaya takarar shugaban kasa a APC.
- Mamakon ruwan sama ya sa dalibai rasa jarabawar JAMB a Legas
- Gwamnan CBN ya sayi fom din Takarar Shugaban Kasa a APC
A ranar Juma’a ne Sanata Yarima ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya ba shi kwarin guiwar shiga takarar.
Adamu, ya ce Sanata Yarima na da matukar muhimmanci ga mutane daban-daban a Najeriya don haka suka zabi ba da gudummawar kudi don saya mishi fom don nuna goyon bayansu ga yunkurinsa na neman ya gaji Shugaba Buhari a 2023.
“Mun yi imanin Yarima shi ne zabin da ya dace. Zai canza abubuwa masu tarin yawa da zarar ya zama shugaban kasa.
“Mun sayi fom din ne domin Yarima ya tsaya takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC,” in ji Adamu.
Wani shugaban YSO na kasa, Farfesa Vitalis Orikeze Ajumbe, ya ce sun bayar da gudumawar ne don kashin kansu duba da cancantar Yarima.
Da yake karbar fom din, Sanata Yarima ya ce zai yaki matsalar tsaro, sannan ya bayar da ilimi kyauta tun daga firamare zuwa sakandare da kuma kafa ma’aikatar harkokin addini idan ya zama shugaban kasa a 2023.
Ya ce, “Na yi farin cikin karbar fom din nan a yau. A matsayina na tsohon gwamna kuma Sanata, na san matsalolin da ke addabar Najeriya, kuma zan magance su cikin nasara.”
Kazalika Yarima, ya ce zai dauki karin ’yan sanda da kuma tabbatar da ba su albashi mai gwabi idan ya zama shugaban kasa.
“Zan magance talauci ta hanyar tabbatar da cewa kowane dan Najeriya yana da abin da zai yi idan na zama shugaban kasa. Dole ne kowane yaro ya je makaranta.
“Zan ba da ilimi kyauta tun daga firamare zuwa sakandare.
“Duk dalibin da ke makarantar gaba da sakandare zai samu kudin biyan kudin makaranta.
“Zan kafa ma’aikatar harkokin addini, limamai za a ba su ikon ilimantar da jama’a kan fahimtar juna a addini da zaman lafiya.
“Kowane dan Najeriya zai sami ’yancin yin addini ciki har da masu son sauya addininsu.
“Zan yaki matsalar tsaro, talauci da jahilci, zan kafa ma’aikatar harkokin addini kuma nan ba da jimawa ba, zan bayyana ra’ayina game da Najeriya,” a cewar Yarima.