✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

A duba cancanta wajen zaben shugabanni a 2023 —Isaac Idahosa

Idahosa ya ce Kwankwaso ne kadai amsa ga matsalolin Najeriya.

Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Isaac Idahosa, ya bukaci ‘yan Najeriya da su duba cancanta wajen kada kuri’a a zaben shugabanni na gari a 2023.

Idahosa ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba lokacin da yake jawabi a garin Minna, babban birnin Jihar Neja.

Idahosa, ya tabbatar da cewa duka jam’iyyun APC da PDP sun gaza, inda ya jaddada cewa mafita daya tilo da za a bi don ceto kasar nan daga halin da take ciki shi ne zaben jam’iyyar NNPP.

Ya shaida wa masu kishin jam’iyyar da sauran mutanen da suka halarci taron cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne mutum daya tilo da zai warware matsalolin ‘yan Najeriya kasancewarsa jagora mai kishin kasa da rikon amana wanda ci gaban kasar nan kadai ne burinsa.

A cewar Idahosa, wadannan halaye ne suka sanya shi amincewa da tayin zama abokin takarar Kwankwaso.

Idahosa, ya jaddada cewa rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, yarjejeniya ce wadda dole ne a mutunta don tabbatar da an yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Sannan ya koka kan yadda ake bin kasar nan bashin sama da Naira tiriliyan 42, wanda a cewarsa bashin na iya shafar rayuwar ‘ya’yan da za a haifa nan gaba.

Idahosa ya yi alkawarin cewa idan aka zabe jam’iyyar NNPP, ya ce za su dauki mutum miliyan daya aikin soja da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro tare da bayar da jarrabawar WAEC, NECO da NAPTEP kyauta ga daliban kasar nan.

Da yake jawabi a wajen taron, dan takarar gwamnan Jihar Neja a karkashin jam’iyyar NNPP, Ibrahim Sokodeke, ya ce ‘yan Najeriya sun yi hankali domin mutum suke bi ba jam’iyya ba.

Sokodeke ya ce shi a nasa bangaren, a shirye yake ya sauya labarin aikin da gwamnati a jihar ta yi, inda ya kara da cewa zai bunkasa Jihar Neja ta hanyar inganta rayuwar al’ummar.