Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ziyarci Hajiya Aya Dada Yar’adua, mahaifiyar tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’Adua, a Katsina.
Wike, wanda ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya ziyarci mahaifiyar Yar’Adua ne a ranar Talata, tare da tsohon Gwamna Katsina Ibrahim Shema.
- Sojoji sun tsere bayan harin ISWAP a Chibok
- Yadda Osinbajo da Babbar Jakadar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing suka halarci Hawan Daushe
Yar’Adua ya rasu shekara 12 da ta gabata. Wike ya kai ziyarar ce a Katsina domin ganawa da wakilan jam’iyyar PDP gabanin zaben fitar da takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
A cikin wani bidiyo na dakika 25, an ga Wike yana gaisawa da mahaifiyar Yar’Adua, inda ya mata sallama “salam alaikum”, ita kuma ta amsa da “Wa-Alaikum-Salaam.”
Dattijuwar wadda ta yi magana da harshen Hausa, kamar yadda Shema ya fassara wa Wike, ta gode wa gwamnan na Ribas da ziyarar da ya kai mata.
Kazalika, Wike ya kuma ziyarci gwamna Bello Aminu Masari na Jihar Katsina.
Wike ya ce ya kai ziyarar ne a hukumance don neman goyon bayan Gwamna Masari bisa aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Masari, a lokacin da yake mayar da jawabi, ya yi kira ga ’yan siyasa a fadin Najeriya da su yi siyasa ta yadda al’umma da harkokin siyasa za su ci gaba da wanzuwa.
Masari ya kuma yaba da irin rawar da Wike ya taka wajen hana kungiyar IPOB shiga Jihar Ribas a lokacin da ake cikin mawuyacin hali.
Har wa yau, ya yaba mishi kan bayar da gudummawa sosai wajen bunkasa harkokin siyasa a Najeriya.