Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yi gargadin cewa tsarin karba-karba zai iya samar wa da Najeriya baragurbin ’yan takarar Shugabancin Kasa a 2023.
Yanzu haka dai muhawara a kan tsarin na karba-karba na ci gaba da yin zafi a Najeriya, musamman yadda zabukan 2023 ke dada karatowa.
- Yadda Ronaldo ya shafe awa 7 a layin shan mai a Burtaniya
- Mahangar Zamani: BBC Hausa ya bullo da sabon shirin mata da matasa
Yayin da Gwamnonin Kudancin kasar suka dage dole sai mulkin ya koma yankinsu, su kuwa takwarorinsu na Arewa sun ce tsarin ba ya cikin Kundin Tsarin Mulki.
To sai dai yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise, Sanusi ya ce tun tale-tale dama yana adawa da tsarin na karba-karba.
Ya ce a yanzu haka, abin da Najeriya ta fi bukata shi ne shugaban da zai kai ta ga tudun mun tsira.
“Na jima ina adawa da wannan tsarin na la’akari da yankin da mutum ya fito. Kowanne yanki ya ja daga dole sai shugaba ya fito daga bangarensa, ko kun lura cewa babu wanda yake magana a kan cancanta kuwa?
“Shi yasa muddin muka ci gaba a haka, akwai yuwuwar mu sami lalatattun shugabanni a matsayin ’yan takara. Duk wanda yake da sha’awar yin takara kawai ya fito, ko daga Kudu yake, ko Arewa.
“Muna da muhimman batutuwa a gabanmu, ga batun aike wa da sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa wanda zai tsaftace harkar zabe, amma wani yana cewa bai yarda da shi ba, yana nuna wa duniya karara cewa yana son yin magudi, ba kunya ba tsoron Allah. Me yasa ba ma magana a kan wannan?
“Ku fito mana da Shugaban Kasa wanda ya cancanta, ko daga wanne bangare yake, za mu zabe shi. Ai ba garinsu zai kai kujerar ba,” inji Sanusi.
Sai dai ya ce ko da yake yana kalubalantar tare kudaden kasa a hannun Gwamnatin Tarayya, Gwamnonin da suke sukarta kan rike kudaden su ma suna da makamanciyar wannan matsalar tsakaninsu da Kananan Hukumomi.