Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce idan ba a zabi ’yan takarar da suka dace ba a Zaben 2023 da ke tafe, laifin masu kada kuri’ar ne.
Ya ce halin da ake ciki a Najeriya ya kai matakin da ya kamata mutanen kirki da suka dace su sa baki domin ceto kasar.
- Tsohon dan wasan Barcelona, Maxi Rolon ya mutu a hatsarin mota
- Tsoron Tsigewa: Buni Ya Bai wa ’Yan Majalisar Yobe Tikitin Zarcewa
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP a Calabar, babban birnin Jihar Kuros Riba, yayin da suke shirin tunkarar zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 28 ga watan Mayun 2022.
Ya ce, “Tarihi zai kafa mana hujja idan har muka kasa zabar wadanda suka cancanta a mukamai.
“Ni a shirye nake, na cancanta, kuma ina da sahihiyar shaidar da suka sa na ba da kaina na shiga cikin masu son ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kanta.”
Tsohon mataimakin Shugaban Kasar ya yi zargin cewa, jam’iyyar APC mai mulki a kasar ta gaza a fannin tsaro, wanda hakan ya jefa rayuwar ’yan Najeriya cikin hadari.
Ya ce, yana da kwazo da azama da jajircewa wajen gyara matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar.
“Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta durkushe wa ’yan Najeriya kwarin gwiwa a fannin tsaro. Yankin Arewacin kasar ya fi fama da matsalar. Kada kuma a ci gaba da faruwar hakan nan gaba.”
Ya kuma jaddada cewa, PDP ba za ta ci gaba za yin zaman dabaro a matsayin jam’iyyar adawa ba, yana mai cewa jam’iyyar za ta kwato Jihar Kuros Riba da kasa baki daya.
Waziri Adamawa ya ce idan har ’yan Najeriya suka ba shi damar zama shugaban kasa, zai yi aiki da Majalisar Dokokin kasar domin sake fasalin kasar.
Ya yi alkawarin ba da karin iko ga Gwamnatocin Jihohi da na Kananan Hukumomi.