A ranar Talatar da ta gabata ce tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya jagoranci kaddamar da wata kungiyar siyasa da suka sa wa suna The National Mobement (TNM)a wani abu da ya kira yunkurin ceto Najeriya.
Kaddamar da kungiyar da ya gudana a Abuja ya samu halartar manyan baki daga sassan Najeriya.
- Zuriyar Dantata: Zuriyar da ta fi dukiya a Afirka ta Yamma
- Wadanda suka yi garkuwa da dan basarake a Taraba na neman N120m
Daga cikin manyan bakin, akwai tsohon Ministan Wasanni, Barista Solomon Dalung da Alhaji Buba Galadima da Sanata Grace Bent da Alhaji Tanko Yakasai da Sanata Rufa’i Hanga da Farfesa Rufa’i Alkali da Alhaji Aminu Ibrahim Ringim da sauransu.
Da yake jawabi a wajen taron, Sanata Kwankwaso, ya ce sun shirya hada karfi da karfe ne tare da wadansu masu irin tunanin ciyar da kasar nan gaba domin taimakon kasar baki daya, musamman a bangaren tattalin arziki da tsaro da inganta rayuwar ’yan kasa.
Kafin taron, an yi ta raderadin cewa a taron ne zai sanar da ficewarsa da Jam’iyyar PDP, inda wadansu suka rika cewa watakila TNM din ce jam’iyyar da zai kafa. Sai dai bayan taron ya ce yana nan har yanzu a cikin Jam’iyyar PDP.
A makon jiya ne ya bayyana cewa APC da PDP babu wani abu da za su nuna wa ’yan kasa na a-zo-a-gani.
Kaddamar da kungiyar ta tayar da kura, inda wadansu suke cewa za ta rikide ta zama jam’iyya nan gaba.
Tuni wadansu daga cikin magoya bayan Kwankwaso suke cewa duk inda ya je za su bi shi, wanda hakan ke nuna cewa jagoran Kwankwasiyar zai iya canja jam’iyyar domin samun tikitin takarar Shugaban Kasa.
Sai dai wadansu suna ganin cewa kamar ya makara, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyya ya yi takara a cikinta, yayin da kuma wadansu suke ganin za ta iya zama jam’iyyar da wadanda suka gaji da PDP da APC za su shiga musamman ganin irin farin jinin da Kwankwason yake da shi musamman a Arewa.
Da yake bayyana ra’ayinsa kan sabuwar kungiyar, tsohon Mai ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Shawara kan Al’amuran Majalisar Wakilai, Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne ya ce, “Ina goyon bayan wannan tafiya saboda za ta farfado da dimokuradiyya da shugabanci nagari da sauran manyan nasarori,” kamar yadda sanarwar da ya fitar ta nuna.
Kawu Sumaila ya kara da cewa zai goyi bayan duk wata tafiya da za ta karfafa dimokuradiyya kafin babban zaben 2023, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin da ke tsakaninsa da wadansu ba.
Ya ce wadanda suka kirkiro Kungiyar TNM mutane ne da suka dade kuma suke kwarewa a siyasa.
Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP, Farfesa Rufa’i Alkali ya shaida wa BBC cewa, “Ai APC ma a shekarun da suka wuce ba a san ta a Najeriya ba, a kankanin lokaci da Allah Ya sa za su yi tasiri suka fito ana zaginsu ana kushe su ana cewa ba za su yi tasiri ba, amma a idon jama’a suka yi tasiri har suka yi mulkin Najeriya.
“PDP kanta lokacin da ta fito a zamanin mulkin soja, ai ana ganin hadari ne a ce za ka dubi Shugaban Kasa na soja ka ce za ka kwace mulki a hannunsa; amma PDP ta yi shugabanci. Sai dai yawanci bayan sun samu mulki kowa ya manta mafari, kuma ba a hangen gaba,” inji Farfesa Alkali.
A nasa bangaren, Kabiru Sa’idu Sufi, malami a Sashin Koyar da Harkokin Siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa sabuwar kungiyar siyasar ta aike da sako mai karfi ga manyan jam’iyyun siyasar kasar nan.
Ya ce: “Tagomashin wannan kungiya ya dogara ne ga irin karfin da za ta kara yi nan gaba; kamar yadda muka gani yanzu, tuni wadansu manyan ’yan siyasa suka shiga cikinta don haka idan aka samu karin ’yan siyasa suka shiga, za ta samu karin tagomashin da zai sa ta yi tasiri.”
Wani matashin dan jarida Aliyu Dahiru Aliyu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa yana da ra’ayin ganin Kwankwaso ya tsaya a PDP.
A cewarsa, “Duk da cewa Kwankwaso yana da matukar farin jini Arewa maso Yamma, zai fuskanci kalubale wajen samun nasara a kasa baki daya idan ya bar PDP, musamman idan ya koma sabuwar jam’iyya. Yanayin zai yi kama da lokacin da Buhari ya koma CPC da lokacin da Atiku ya koma ACN kafin su hade daga baya.”
Aliyu ya kara da cewa, “Kwankwaso har yanzu yana da matukar mutunci da magoya baya a siyasar Kano, kuma zai iya tsayar da dan takara a Kano ya samu nasara a kowace jam’iyya, sai a samu irin yadda aka samu a Anambra da APGA ta samu nasara duk da kasancewar APC da PDP. Amma a ra’ayina, ina so Kwankwaso ya tsaya a PDP domin ci gaba da samun tagomashi a siyasar kasar baki daya.”
Aliyu ya kara wallafa wani rubutun, inda ya ce, “In dai da manufar ci gaba ake siyasa to tabbas Kwankwaso ya yi an gani a Jihar Kano. Amma akwai masu siyasa saboda neman na abinci, wadannan kuma ba ka hana su neman ba. Ni dai ina sha’awar koma wa zai mulki kasar nan to ya yi abin da Kwankwaso ya yi a Kano don talakawa su amfana.”