Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kafa kwamitin mutum 37 da zai yi aiki wajen warware takaddar tsayawa takarar kujerar Shugaban Kasa karkashin inuwar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa.
Wasu daga cikin mambobin kwamitin sun shaida wa manema labarai cewa, sun shirya yadda za su kawo karshen takaddamar yakin da zai fitar da dan takarar da zai tsaya wa jam’iyyar a zaben 2023.
- Kar a zabi masu ikirarin an saya musu tikitin takara —Obasanjo
- Majalisar Wakilai za ta tsunduma yajin aiki saboda matsalar tsaro
Jam’iyyar PDP na cikin rikici inda ’ya’yanta daga shiyyoyin kasar ke neman tsayawa takara, kuma kowane yaki aminta tare da bar wani daga cikinsu takarar.
Domin shawo kan lamarin, PDP a taronta na 95 na Kwamitin Zartarwa na Kasa da ta gudanar a ranar 16 ga watan Maris, ta kafa kwamitin da zai wanzar da zaman lafiya.
Kwamitin wanda gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ke jagoranta, ya samu wakilcin mambobinsa a fadin kasar nan da suka hada da gwamnoni uku da tsofaffin gwamnoni 12 da tsofaffin ministoci da ‘yan majalisu.
Kwamitin ya gudanar da taro sau biyu domin lalubo hanyar da za a bi wajen ganin an shawo kan matsalar ba tare da kowa daga Arewa ko Kudu ba.
Wani dan kwamitin ya ce sama da rabin ’yan kwamitin sun sanya hannu kan tsarin bai-daya domin bai wa duk masu son shiga zaben fid da gwani dama.
Saraki, Tambuwal, Bala sun gana da IBB a kan yarjejeniya
’Yan takarar Shugaban Kasa uku na jam’iyyar PDP daga Arewa; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki; Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na Jihar Bauchi, Bala Mohammed sun gana da tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kan bukatar jam’iyyar ta dauki dan takararta a gabanin zaben fid da gwaninta.
Mutanen uku dai sun yi ta fadi-tashin ganin an amince da dan takarar shugaban kasa guda daya domin kawo karshen takun saka a jam’iyyar.
Da yake jawabi, Saraki ya ce sun ziyarci IBB ne don neman shawararsa a matsayinsa na jagora a kan hanyar da za a bi domin cimma matsayar da aka tsara.
“Muna kan hanyar neman shawarwari daga shugabanninmu da masu ruwa da tsaki na PDP. Mu ’yan takarar jam’iyyar PDP mun ga ya dace mu zo mu yi wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja bayanin abin da mu ke ciki dangane da yarjejeniyar da ake son cim ma.
“Mun yi haka ne don tabbatar da cewa tsarin ya tafi daidai. Muna bukatar goyon bayan shugabannin jam’iyyar da shawarwarinsu,” inji shi.
Da ya ke mayar da martani, Babangida ya ce ya yi farin ciki da shawarar da aka cimma, wanda a cewarsa hakan zai samar da zaman lafiya da hadin kan kasar nan.
“Na ji dadin haduwa da ku. Hadin kan kasar nan shi ne mafi muhimmanci. Na san samun ingantacciyar Najeriya shi ne babban burinku. Kuma hakan ba zai samu ba matukar babu hadin kai da masalaha,” in ji IBB.
’Yan takara 13 sun sayi fom din takara a PDP
Ya zuwa yanzu, akalla mutum 13 ne suke neman tsayawa jam’iyyar takarar Shugabancin Kasa a 2023, daga Kudanci da Arewacin Najeriya.
Hakan ya sa mutane da dama na tambayar ko jam’iyyar ta yi watsi da tsarin karba-karbar da aka san ta da shi a baya.
Daga cikinsu akwai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim.
Kazalika, akwai Gwamnoni guda hudu; Bala Mohammed (Bauchi), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato), Udom Emmanuel (Akwa Ibom) da Nyesom Wike (Ribas) suma sun biya miliyan 40 don sayen fom din takarar.
Sauran sun hada da tsohon dan jarida kuma mawallafi, Dele Momodu, dokta Nwachukwu Anakwenze, Mazi Sam Ohuabunwa, tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi da wani ma’aikacin banki Mohammed Hayatu-Deen (mai ritaya).
Diana Oliver Tariela, ita ce mace daya tilo da ta sayi fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar a kan kudi miliyan biyar.