✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Osinbajo ya sayi fom takararsa a APC na N100m

Sanata Kabiru Gaya ne ya sayi fom din a madadin Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya sayi fom din takarar Shugabancin Kasa karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Daya daga cikin jagororin yakin neman zabensa, Sanata Kabiru Gaya ne ya karbi fim din a madadin Osinbajon ranar Alhamis.

Osinbajo dai ya bayyana aniyarsa ta neman takarar a watan Afrilu inda tuni kuma ya dukufa zagayen ji ta bakin daliget-daliget gabanin gudanar da zaben cikin gidan jam’iyar da za ayi a karshen watan Mayu.

Jam’iyyar ta APC dai ta kara kwanaki hudu a wa’adin siyar da fama-faman.

Za a gudanar da zaben fid-da gwanin Shugaban Kasa na jam’iyyar ranar 30 ga watan Mayun 2022.