Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce lokaci ya yi da ’yan Arewa za su nuna goyon baya ga jagorar jam’iyyar APC mai neman takarar shugabancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Shettima ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Aminiya a ranar Lahadi, inda ya jaddada cewa wannan lokaci ne da ya kamata a yi wa Tinubu sakayyar wahalar da ya yi na cika dogon burin shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari bayan ya tika Shugaba Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP da kasa.
- ’Yan bindiga sun huce fushi kan masu ba wa jami’an tsaro hadin kai
- Macron na fatar kawo karshen tankiya tsakanin Rasha da Ukraine
Tsohon Gwamnan na daya daga cikin gwamnonin tsohuwar jam’iyyar ANPP uku da suka koma APC bayan rugujewar tasu jam’iyyar lokacin gamayyar da aka yi ta jam’iyyu a zaben 2015.
Sanata Shettima ya ce Tinubu ne ya shige gaba aka yi duk wani fadi-tashi don ganin Shugaba Buhari ya hau mulki, don haka a yanzu ya cancanci a ramawa kura aniyyarta.
Ya ce gabanin ya goyi bayan Buhari a 2015, Tinubu da ke zaman tsohon gwamnan Jihar Legas ya yi watsi da ta sa aniyyar wajen goyon bayan takarar wasu yan Arewa biyu — tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzki Zagon Kasa ta EFCC, Nuhu Ribadu.
Tsohon gwamnan na Jihar Borno ya ce Tinubu ya goyi bayan ’yan Arewan biyu a lokuta daban-daban duk da kuwa yana da duk wata cancantar tsayawa takara a wadannan lokuta.
An yi amannar cewa Buhari da Tinubu su ne mutum biyu da suka fi kowa mahimmanci a tafiyar APC a 2015, wanda gamayyarsu ta kai ga Buhari ya samu shugabancin Najeriya.
“Babu shakka Buhari na da farin jini a Arewa. Akwai mabiyansa kusan miliyan 15 a yankin. Amma hakan bai sanya ya zama shugaban kasa ba sai da ya hada hannu da ’yan siyasar sauran bangarorin Kudanci da sauran yankuna aka sauya masa fasali tukunna ya zama shugaban kasa a 2015,” in ji Shettima.
Ana iya tuna cewa, an kirkiri jam’iyyar APC a sakamakon gamayyar da aka yi tsakanin jam’iyyun ACN, ANPP, wani tsagi na jamiyyar APGA da kuma sabon tsagin jam’iyyar PDP (nPDP).
Dangane da ko akwai wata yarjejeniya da aka kulla tsanakin Buhari da Tinubu, Ssnata Shettima ya ce, “a gani na Tinubu yana da masaniyar cewa babu wani abun dogaro a kan duk wata yarjejeniya da aka kulla a siyasance musamman a irin wannan yanayi mai tazarar shekaru hudu ko takwas masu zuwa.
“Ko da mako daya ne a siyasa, lokaci ne mai tsawo don babu wanda zai iya hasashen mai zai faru daga yanzu zuwa 2023 ballantana kuma idan aka koma shekarar 2015.
“A siyasa babu wani abu mai garanti face wanda yake kusa da kai wanda babu wani shamaki na lokaci a tsakani.”