Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli na Harkokin Musulunci na Najeriya (NSCIA), Muhammadu Sa’ad Abubakar III da takwaransa na Kungiyar Kiristoci na Najeriya (CAN), Archbishop Daniel Okoh, sun yi kira ga ’yan Najeriya kan su zabi abin da za suka natsu da shi a zabe mai zuwa don samun zaman lafiya a kasa.
Sun yi kiran ne a wajen taron da Majalisar Kawancen Addinai (IDFP) ta gudanar ranar Laraba mai take: ‘Addini da Kabilanci: Kare Babban Zaben 2023.’
A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya jaddada bukatar a hada kai don ci gaban kasa wanda a cewarsa, hakan ba zai samu ba sai da zaman lafiya da tsaro da hadin kan ’yan kasa.
“Za mu amfana matuka idan muka hada kanmu, da farko mu sanya kasarmu gaba kafin kabila,” in ji shi.
Ya kara da cewa kowa ya je ya karbi katin zabensa sannan a tafiyar da komai cikin lumana lokacin zabe, kana a zabi cancanta, a bar wa Allah sauran.
A nasa bangaren, Shugaban CAN, Daniel Okoh a bisa wakilcin Rabaran Benebo Fubara-Manuel, ya ce “Ubangijinmu na gaba da komai namu, don haka dole mu saurare Shi mu yi maSa biyayya.
“Mu sani cewa Allah kadai zai iya ba mu shugabanni nagari, amma dole mu zabi cantanta ba tare da nuna bambancin kabila ko na addaini ba,” in ji shi.
Da yake jawabi a wajen taron, Dokta Saidu Ahmed-Dukawa na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ya ce bambancin addini da kabilanci yana da kyau, sai dai ana amfani da su wajen magudin zabe a Najeriya.