✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Kotu ta umarci INEC ta ci gaba da rajistar masu zabe

Kotu ta ce INEC ta gaggauta ci gaba da yi wa masu zabe rijista har zuwa 90 kafin zaben 2023.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) umarnin ta gaggauta komawa ta ci gaba da shirin yi wa masu zabe rajistar zaben 2023.

Umarnin kotun ya nuna INEC za ta koma ta ci gaba da shirin ne har sai ya rage kwana 90 kafin zaben na 2023.

Cikin hukuncin da ya yanke ranar Talata, Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya bai wa INEC umarnin ta tabbatar ba ta hana dukkan ’yan Najeriya da shekarunsu ya kai 18 damar yin rajistar ba.

Ya ce hakki ne a kan INEC ta tabbatar da ta yi shirye-shiryen da suka kamata daidai da doka wajen gudanar da shirin.

Alkalin ya ce, “Karar ta samu nasarar ne saboda cancanta.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa Anajat Salmat da wasu mutum uku ne suka shigar da kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/1343/2022 a kan INEC inda suka nemi a ci gaba da shirin yi  wa jama’a rijistar zabe.

Sun bukaci hakan ne domin bai wa dandazon ’yan kasa da ba su samu yin rajista ba damar yin haka, kasancewar da sauran lokaci kafin babban zaben 2023.

(NAN)