✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

2023: Kotu ta kori dan takarar gwamnan APC a Ribas

Ana zargin Cole da samun shaidar dan kasa guda biyu na kasashe daban-daban.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta kori dan takarar gwamnan Jihar Ribas na jam’iyyar APC, Tonye Cole, saboda samunsa da shaidar zama dan kasa biyu mabambamta da kums karan-tsaye da jam’iyyarsa ta yi wa Dokar Zabe.

Jam’iyyar PDP a jihar ce ta garzaya kotu domin a bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) umarni kin amincewa da Mista Tonye Cole a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin yana da shaidar dan kasa guda biyu.

PDP ta kuma yi zargin cewa wakilian jam’iyyarsa ba su bi ka’ida ba wajen zabarsa.

Alkalin kotun, mai shari’a Emmanuel Obile a hukuncin da ya yanke, ya amince da batun jam’iyyar PDP cewa Mista Cole wanda ke da shaidar dan kasa biyu bai cancanci tsayawa takarar gwamna ba da kuma zaben fid-da-gwanin jam’iyyar APC da ya kawo shi.

Tuni kotun ta bai wa jam’iyyar umarnin sake wani zaben fid-da-gwanin a jihar.