✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Jam’iyyun Kano sun ki fara kamfe, mako 1 bayan kada gangar siyasa

APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta NNPP a Jihar Kano sun koma cacar baka ta kafofin yada labarai, maimakon yakin nema zabe gadan-gadan

Mako guda bayan kada gangar siyasar zaben 2023, amma har yanzu manyan jam’iyyun siyasa a Jihar Kano ba su fara yakin neman zabe ba.

Aminiya ta lura tun bayan da Hukumar INEC ta janye takunkumin yakin neman zabe, Jami’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta NNPP a Jihar Kano sai cacar baka suke ta yi a kafofin yada labarai, maimakon yakin nema zabe gadan-gadan yadda aka saba.

Cacar bakan tsakanin manyan jam’iyyun siyasar ta samo asali ne daga zargin da APC ta yi wa NNPC da tsageranci da kuma aikata muggan ayyuka a jihar.

ِِAPC ta zargi magoya bayan NNPP da kai hare-hare tare da kwace wa mutane wayoyi a lokacin da ta kaddamar da ofishinta na yakin neman zabe a jihar.

Kwamishinan Yada Labran Jihar Kano, Muhammada Garba, wanda shi ne kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Takara Gawuna/Garo a kujerar gwamnan jihar a APC, ya zargi magoya bayan NNPP da kai wa jama’a hari da kuma kwacen wayoyi, maimakon bude ofishin nasu da suke yi.

Amma a martaninta, NNPP ta kalubalanci gwamnatin APC ta jihar da ta gabatar da sunayen mutanen da aka kashe a lokacin taron bude ofishin yakin neman zaben.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben NNPP na jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce zargin da APC ba shi da tushe, hasali ma wani yunkuri ne boye mummunan abin da jam’iyyar take kitsawa domin zaben da ke tafe.

A sanarwarta ta fara yakin neman zaben 2023, NNPP ta ce ba za ta lamunci wani zaben da bai kammalu ba kamar yadda aka yi a 2019 a jihar.

Amma a martanin APC, ta ce miyagun ayyukan mambobin NNPP wadanda a 2019 suke PDP ne ya haifar da sanar da sakamakon zaben cewa bai kammalu.

Ta ce don haka sai su kiyayi yin magudi da aringizon kuri’u a zaben da ke tafe.