Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta ce hare-haren da ake kai wa ofisoshinta da ma ma’aikatanta ba za su hana ta gudanar da babban zaben 2023 cikin nasara ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka (AU), karkashin jagorancin Phumzile Mlambo-Ngcuka, ranar Litinin a Abuja.
- An fara ba ma’aikata mazan da matansu suka haihu hutun kwana 14 a Najeriya
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
Yakubu ya ce tuni an yi asarar wasu kayan aikin da aka tanada don zaben na 2023 sakamakon hare-haren da aka kai ofishin INEC a wurare daban-daban a fadin kasar.
Ya ba da tabbacin hukumar za ta sake mallakar kayayyakin da asarar ta shafa kafin zaben.
Ya kara da cewa, duk da nasarorin da INEC ke samu wajen shirye-shiryenta, fannin tsaron kasar abin damuwa ne, musamman hare-haren da ake kai wa ofisoshin hukumar.
Ya ce a cikin mako ukun da suka gabata, an kai wa ofishinsu hari a wasu Kananan Hukumomi uku a jihohi daban-daban.
Tun farko da yake jawabi, shugaban tawagar Mlambo- Ngcuka, ya ce sun zo Najeriya ne domin nuna goyon baya ga kasar dangane da zaben da za ta gudanar a 2023.