Bayanai na nuna cewa bisa ga dukkan alamu, Gwamnonin APC na son Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauki daya daga cikinsu a matsayin dan takarar jam’iyyar, maimakon bin tsarin karba-karba.
An kara fahimtar hakan ne sakamakon karin bayanan da suka bayyana yayin taron da Shugaba Buhari ya yi da ilahirin Gwamnonin APC kwanan nan a Abuja.
- In ba don ni ba Buhari ba zai ci zabe ba a 2015 — Tinubu
- Kasar Turkiyya ta sauya sunanta a hukumance
Yayin taron nasu, Shugaba Buhari ya bukaci Gwamnonin su ba shi damar zaben wanda zai gaje shi bayan kammala wa’adin mulkinsa.
Jaridar PUNCH ta kalato cewa, kawo yanzu, Gwamnonin na APC sun yi taro sau biyu, inda ake sa ran su sake yin wani taron kafin ko ranar Asabar.
Majiyar Aminiya ta ce, yayin zaman Gwamnonin na farko, sun tattauna ne kan yiwuwar su zabi dan takara a tsakaninsu kamar yadda Buhari ya bukata.
“Da dama daga cikin Gwamnonin sun yarda cewa wannan batun abin a jaraba ne,” kamar yadda wata majiya ta kusa da taron ta shaida wa Punch.
Zaman Gwamnonin na biyu kuwa ya mayar da hankali wajen tattauna wanda ya fi cancanta su yi masa mubaya’a a matsayin dan takarar APC.
PUNCH ta gano cewa batun shiyya shi ne ya mamaye zaman tattaunawar gwamnonin na biyu, inda wasu gwamnonin Arewa ke ganin cewa dan Arewa ne ya fi dacewa a dauko a yi masa mubaya’a a matsayin dan takarar APC.
Duk da dai majiyar ba ta ambaci wani Gwamnan Arewar da ake ganin shi zai fi cancanta zama magajin Buharin ba, amma abin sani shi ne Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da takwaransa na Jigawa, Mohammed Badaru suna cikin jerin ’yan takarar Shugaban Kasa a karkashin APC.
Sai dai majiyar ta ce, wannan batu ko tsari bai yi wa Gwamnonin Kudu maso Yamma, irin su Rotimi Akeredolu da sauransu daɗi ba, saboda nan take suka nuna hakan ba za ta sabu ba.
Game da batun takarar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu kuwa, majiyar ta ce galibin muhawarar da aka tafka a zaman ta ta’allaka ne a kan wanne Gwamna ne zai fi dacewa ya zama magajin Buhari. Yayin da su kuma Gwamnonin Kudu suke magana a kan tsarin karba-karba.
Duk da dai Gwamnonin Kudu na kwadayin a ce mulkin ya koma wajensu, amma takwarorinsu na Arewa suna ra’ayin cewa da wahalan gaske a iya kayar da dan takarar PDP, wato Atiku Abubakar a zabe mai zuwa muddin aka tsayar da dan Kudu a matsayin dan takarar APC.
Atiku dai dan asalin Jihar Adamawa ne daga Arewacin Najeriya wanda ya yi takarar neman zama Shugaban Kasa har sau biyar, wato a 1993, da 2007 da 2011 da 2015 da kuma 2019.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, yadda sakamakon zaman Gwamnonin na gaba zai kasance, da kuma shin ko za su iya cin ma matsayar tsayar da mutum guda daga cikinsu, dan Arewa ko kuma daga Kudu?